
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Alhamis Majalisar Dattawa ta sanar da nesanta kanta daga sammacin kama tsohon Shugaban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), Mele Kyari, wanda Kwamitin Majalisar kan kuɗaɗen al’umma ya bayar.
Haka kuma, Majalisar ta bakin jagoran masu rinjaye, Sanata Bamidele Opeyemi, ta bayyana cewa kalaman da aka danganta ga Sanata Adams Oshiomhole, mai wakiltar Edo ta Arewa ba su wakiltar matsayar shugabancinta.
An ce Oshiomhole ya bayyana NNPC a matsayin “gungu na masu laifi da ɓarayi” yayin zaman kwamitin a ranar Laraba, amma Majalisar Dattawa ta yi watsi da danganta waɗannan kalamai da ita baki ɗaya.
Lamarin na zuwa ne yayin da ake cigaba da bincike da sauraron bayanai akan harkokin NNPC da wasu batutuwan kuɗaɗen jama’a.
A baya an aike wa Kyari saƙon gayyata a lokuta da dama akan ɓatar wasu, maƙudan kuɗaɗe da jimillarsu ta kai Naira tiriliyan 210 da ba a bayyana yadda aka yi amfani da su ba, amma tsohon shugaban ya yi buris da kiraye-kirayen.
