Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina
Gwamnan jihar katsina Malam Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da gidaje 152 na ‘yan gudun hijira da hukumar UNDP da haɗin gwiwar gwamnatin katsina suka gina a garin Jibiya a ƙaramar hukumar Jibiya.
Haka Kuma hukumar UNDP ta gina asibitin dabbobi da cibiyar samar da zanan da magance sauyin yanayi duk da kasuwar zamani.
Dikko ya ce sun kuma samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a ƙauyuka ƙaramar hukumar Jibiya da asibitin dabbobi.
Sura sun haɗa da gina manyan shaguna da ƙananan da wuraran ba haya, kasuwar dabbobi da sauran su.
A jawabinsa gwamna Dikko Raɗɗa ya ce ba wai gina gidajen kawai aka ba ‘yan gudun hijira ba,”za a basu gadaje da katifu,kayan girke girke da buhun shinkafa gami da kudi dalar Amurka 200 ga kowanne mutum da ya mallaki gidan domin da samu natsuwa,”Inji gwamnan.
Malam Dikko Radda ya ƙara da cewa gwamnatin katsina ta kuma gina magudanan ruwa da hanyoyi, wajen gudanar da Ibada da makarantu.
Haka kuma gwamnatin Katsina ta tallafa wa mutane 500 da kudi dalar Amurka miliyan dari biyar da masu kabanan sana’o’i a garin Jibiya domin farfaɗo da ƙananan sana’o’in su da ya durƙushe sakamakon hare haren ‘yan bindiga a lokutan baya.
Kan haka gwamnan ya yi Kira da yan bindiga da ke daji da su aje makaman su,su shigo cikin Yanuwansu a karkara domin su cigaba da rayuwa yadda yan uwansu suke a karkara.
Dikko ya ce kofar sa a buɗe yake domin tattaunawa da tuba domin tabbatar da zanan lafiya a jihar.
Suma jakadun ƙasashen Jamus da Norwey da Kuma wakiltar UNDP sun yabawa gwamnatin Katsina kan yadda ta ke tafiyar da harkar tsaro ƙarƙashin gwamna Dikko Radda.
Kuma sun nan kudirin su na cigaba ma gwamnatin katsina wajen jawo zanan lafiya da cigaban jihar.
