Nijeriya da Amurka sun faɗaɗa haɗin gwiwar yaƙi da ta’addanci – Hedikwatar Tsaro

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya (DHQ) ta bayyana cewa Nijeriya da Amurka sun ƙara zurfafa haɗin gwiwarsu ta fuskar tsaro, inda haɗin kan ya wuce musayar bayanan sirri da horar da jami’ai, zuwa gudanar da ayyukan soji na bai ɗaya domin yaƙar ƙungiyoyin ta’addanci, musamman a yankin Arewa maso Gabas.

Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Manjo Janar Samaila Uba, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta kai-tsaye a shafin ɗ mai taken “ƙarfafa Tsaro Ta Hanyar Musayar Bayanai Cikin Hikima: Haɗin Gwiwar Sojojin Amurka Da Nijeriya A Yaƙi Da Ta’addanci.” Taron ya haɗa da wakilan Rundunar Sojojin Nijeriya, Rundunar Sojin Amurka Ta Nahiyar Afirka (AFRICOM), jami’an gwamnati, masana harkokin tsaro da sauran jama’a.

A cewar Manjo Janar Uba, sauye-sauyen da ake samu a dabarun ta’addanci da kuma ƙalubalen tsaro na zamani sun sa ya zama wajibi Nijeriya ta ƙara ƙarfafa alaƙarta da ƙawayenta na tsaro.

Ya ce baya ga musayar bayanan sirri da sauran nau’ukan haɗin gwiwa, an gudanar da hare-haren hadin gwiwa kan wasu sansanonin ’yan ta’adda.

“Mun gudanar da wasu hare-haren haɗin gwiwa baya ga musayar bayanan sirri da sauran haɗin kai. Muddin muna buƙatar irin waɗannan ƙwarewa da kayan aiki, za mu ci gaba da aiki tare da abokan hulɗarmu,” inji shi.

Ya bayyana cewa haɗin gwiwar ta taimaka matuƙa wajen inganta tattara bayanan sirri, sa ido kan ayyukan ’yan ta’adda, tsara hare-haren soji da kuma kai farmaki cikin ƙwarewa a wuraren da suke ɓoye.

Daraktan yaɗa labaran ya kuma bayyana cewa daruruwan jami’an sojin Nijeriya na cin gajiyar shirye-shiryen horaswa na musamman da ake gudanarwa a ƙarƙashin haɗin gwiwar tsaron ƙasashen biyu.

A cewarsa, horon ya shafi dabarun yaƙi da masu tayar da ƙayar baya, nazarin bayanan sirri, tsara manufofin tsaro, jagoranci da sauran muhimman fannoni da za su ƙarfafa tsarin tsaron Nijeriya.

“Rundunar Sojojin Nijeriya na amfana ƙwarai daga wannan haɗin gwiwa ta fuskar haɓaka ƙwarewa, horaswa ta musamman, tallafin bayanan sirri da kuma ƙarfafa ƙarfin gudanar da ayyukan tsaro,” inji Uba.

Duk da nasarorin da ake samu a fagen daga, Manjo Janar Uba ya jaddada cewa ba za a iya kawo ƙarshen ta’addanci ta hanyar amfani da ƙarfi kaɗai ba.

Ya bayyana cewa dabarun Nijeriya na yaƙi da ta’addanci sun haɗa da hanyoyin soja da kuma waɗanda ba na soja ba, domin magance tushen matsalar tsattsauran ra’ayi.

“Ba za a iya kawar da ta’addanci da amfani da makami kaɗai ba. Hanyoyi irin su haca kai da al’umma, ƙarfafa tattalin arziki, wayar da kai da kuma magance ƙorafe-ƙorafen jama’a suna da matuƙar muhimmanci,” inji shi.

Ya ƙara da cewa rundunar sojin ta rungumi tsarin da ke haɗa sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, ƙungiyoyin fararen hula da sauran masu ruwa da tsaki domin daƙile yaɗuwar tsattsauran ra’ayi da ƙarfafa zaman lafiya a cikin al’umma.

Ita ma Daraktar Hulɗa da Jama’a ta AFRICOM, Kanal Rebecca Heyse, ta sake tabbatar da cewa Amurka na mutunta cikakken ikon Nijeriya yayin gudanar da haɗɗin gwiwar tsaro.

Ta ce dukkan ayyukan da suke yi a Nijeriya ana gudanar da su ne bisa gayyata da kuma yarjejeniyar da gwamnatocin ƙasashen biyu suka amince da ita ta hannun Kwamitin Haɗin Gwiwar Tsaro Na Amurka Da Nijeriya.

“Haɗin gwiwarmu da Nijeriya ya ta’allaka ne kan cikakken girmama ikon ƙasar. Muna aiki ne bisa gayyata kuma bisa tsarin da ƙasashen biyu suka amince da shi,” inji ta.

Mai magana da yawun Shugaban ƙasa kan harkokin sadarwa, Sunday Dare, ya ce musayar bayanan sirri da haɗin gwiwar ayyukan tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka na daga cikin manyan abubuwan da suka taimaka wajen samun nasarori a yaƙi da masu tayar da ƙayar baya.

Ya bayyana cewa haɗin kan ya taimaka wajen ƙara inganci, sauri da daidaito a ayyukan rundunonin tsaro a wurare daban-daban na rikici.

By ukarofi