Jamilu Gwamna ya yi jimamin rasuwar Yaya Bauchi Tongo

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Ɗan takarar gwamnan jihar Gombe na jam’iyyar APC Dakta Jamilu Isiyaku Gwamna, ya nuna alhini kan rasuwar ɗan majalisar wakilai da ke wakiltar mazaɓar Gombe/Kwami/Funakaye, Yaya Bauchi Tongo.

A cikin saƙon ta’aziyya da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Gwamna ya bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen wakili mai himma da ya riƙa wakiltar mazaɓarsa cikin gaskiya, tawali’u da kuma cikakken nauyin aiki.

Ya bayyana cewa rasuwar Hon. Tongo babban rashi ne ba ga iyalansa da mutanen mazaɓarsa kaɗai ba, har ma ga jihar Gombe baki ɗaya, musamman ma Gombe ta Arewa inda aka san shi a matsayin ɗan siyasar ƙasa da ke da kusanci mai ƙarfi da jama’arsa.

A cewarsa, marigayin ya kasance yana nuna cikakken jajircewa wajen inganta rayuwar al’ummarsa tare da yin aiki tuƙuru don tabbatar da cewa muryoyinsu sun isa a majalisar wakilai ta ƙasa.

Gwamna ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, abokan aikinsa na siyasa da kuma al’ummar mazaɓarsa, yana roƙon Allah maɗaukakin sarki ya gafarta masa kurakuransa tare da masa rahama, ya kuma sanya shi aljannatul firdaus.

By ukarofi

Leave a Reply