Gwamnatin Katsina ta ayyana gobe Talata hutun shiga sabuwar shekarar Musulunci

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta ayyana ranar Talata, 16 ga Yuni, 2026 a matsayin ranar hutu domin bikin fara shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1448AH (1 ga Muharram).

Kwamishinan yaɗa labarai da al’adu na jihar, Dakta Bala Salisu Zango, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin.

Gwamnan ya buƙaci al’ummar jihar su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’o’i da tunani domin samun zaman lafiya, ci gaba da wadata ga Jihar Katsina da Nijeriya baki ɗaya.

By ukarofi

Leave a Reply