
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Yayin da ake cigaba da fafatawa tsakanin ƙasashe daban-daban a Gasar Kofin Duniya na 2026 a satin farkon, ƙasar Sifaniya da ake ganin ka iya lashe kofin, za ta kara da Cape Verde ba tare da ɗan wasa Lamin Yamal ba a sahun farko.
Wannan shi ne karo na farko da Cape Verde ta samu damar shiga gasar tun bayan zama mambar Hukumar Ƙwallon ta Duniya (FIFA) a shekarar 1985.
Kasar ita ce ƙaramar ƙasa ta uku da taɓa nasarar hayewa zagayen shiga gasar ta fuskar yawan jama’a, inda Curacao da Iceland ne sauran ƙananu biyun a na 2018.
A ɗaya ɓangaren, Lamine Yamal ne ɗan shekara 16 na farko a tarihi da ya taɓa shiga gasar Yuros kuma ya zura ƙwallo.
Haka kuma, ‘yan wasa guda bakwai ne kaɗai suka taɓa zura ƙwallo a Kofin Duniya gabanin su kai shekara 19 a tarihi.
Ana ganin wannan karawa za ta yi zafi musamman ganin yadda Cape Verde ke fatan kai wa rukuni na gaba, yayin da wasu daga cikin ‘yan wasan Sifaniya ke fama da rauni.
