Daga ALI ABUBAKAR SADIK
Ya mai karatu, ajiye wannan rubutun a yau, ko da Allah zai karbi Rai na kafin lokacin, to bayan zabe ka dauko shi ka tunawa Duniya ko ka tuna wa kanka hasashe na ya zama gaskiya ko akasin haka. Amma kafin nan, ka saurari hujjoji na wannan hasashe nawa.
Kamar yadda na sha fada a baya, a tarihin zabe a Duniya, duk inda ka ga jam’iyyar adawa ta kayar da Mai mulki, wajibi ne sai ka sami abubuwa guda biyu: Na farko, jam’iyyar adawa mai karfi, sannan na biyu, Dan takara Mai karfi wanda goyon bayansa ya fantsama ko’ina. Musamman a nan Najeriya inda dokar tsarin mulki ta tanadi lallai mai neman shugabancin Najeriya dole sai ya ci kaso 25% na kuri’un da aka kada a jihohi 24 cikin 36 na Najeriya.
Na farko a yanzu a Najeriya babu wata jam’iyyar adawa mai karfin da za ta iya ja da APC, saboda PDP dai kowa ya san ta mutu. ADC baya ga matsalar halascin shugabancin jam’iyya, wanda zai iya zama mata matsala ko an yi zabe, ficewar Obi da Kwankwaso, ya kassara karfinta a kasa. NDC kuma, jam’iyya ce ta bangaren inyamurai domin hatta tsarin shugabancin ta bai nuna kasancewarta jam’iyyar kasa ba, domin inyamurai su ka mamaye mukamanta. Don haka a yanzu dai, babu wata jam’iyyar adawa mai karfin yaduwa da hadakar Yan siyasa a cikinta da za su iya ja da APC a zaben kasa. Wannan shine babban nakasun adawa a Najeriya a yau, kuma shine dalilin da ya sa su ka kasa cin zabe a 2023 duk da kasancewar sun zarta APC da sama da kuri’a miliyan 4.
A zaɓen 2023, Peter Obi ya iya cin wancan kaso 25% ne a jihohi 16 kacal, wato ya Gaza da jihohi 8 kenan. Atiku da ya fi shi karbuwa a sassan Najeriya shi ma a iya jihohi 21 ya iya samo kaso 25% duk da cewa a wancan lokacin PDP ta kasance jam’iyyar adawa mai karfi domin ta na da gwamnoni 13.
A yaƙin neman zabe a 2023, kowa ya ga irin halin da inyamurai su ka nuna wajen goyon bayan Obi, da zage-zage, da nuna bangaranci na kabila da addini. Hatta yawon kamfen na Obi, wato wuraren da ya halarta a Arewa mafi yawa ya maida hankalinsa ga kiristoci. Yakin neman zabensa a kullum na zafafa rarrabuwar Yan Najeriya fiye da hado su kan matsaloli da su ka dame su.
A wannan karon, sakamakon hadewa da Kwankwaso, wanda kungiyarsa ta Yan Kwankwasiyya daidai ta ke da ta Yan Obedients wajen makauniyar biyayya da rashin kunya da zage-zage, ya haifar da cece-cece kuce mafi muni tun yanzu, yadda hatta Sardauna ya zama abin muzantawa. Duk da cewa Sardauna kamar kowa ya na da kura-kurai amma alherinsa ga Arewa bai cancanci irin wannan muzantawa saboda Inyamuri ba.
Akasarin matasa ba su san waye Inyamuri ba. Su ne su ka tsunduma Najeriya cikin masifar bangaranci saboda yadda daga karshen mulkin turawa da farkon yancin Kai, kasancewar sun fi kowa a kasar manya Yan Boko da sojoji, tare da halayyarsu ta mamaya da nuna fifiko, ya iza wutar kabilanci. Su ne su ka fara yin juyin mulki su ka kashe Yan Arewa da Yarbawa. Su ne su ka ja aware, domin kafa kasar Biafra. Su ne su ka jawo yakin basasa. Su ne bayan yaki an murkushe su a filin daga, su ka lashi takobin murkushe sauran Najeriya ta hanyar shigo da fashi da makami, satar mutane, safarar kwaya, da ayyukan 419. Wato a takaice, duk sharrin da Najeriya ta fuskanta a baya, da wanda ta ke fuskanta a yanzu, idan ka bibiyi asalinsa, inyamurai su ka kawo shi.
Idan ka koma yadda al’ummomi a ko’ina cikin Najeriya su ka karbi Inyamuri, shi a kasarsa ko hayar shago ba zai baka ba ballantana fili ka Gina gida. Har gobe Inyamuri ya tsani sauran kabilu, ya raina su, bai yarda da kasar Najeriya ba a zuciyarsa saboda a kullum fafutukar kafa Biafra ce a zuciyarsa. Hatta Yan uwansu na Niger Delta ba sa kaunarsu. Wadannan dalilai na cikin dalilan da ya sa sauran kabilu su ka ki sahalewa Inyamuri mulkin Najeriya tsawon shekaru sama da 50. Duk sanda ake zo siyasa, Inyamuri baya jin kunyar ya fito karara ya nuna kiyayyarsa da kabilanci sa ga kowa. Ita siyasa ta kasa sai ka yarda da mutane sannan zasu yarda da kai. Kuma zabe Dan kuri’a ne, yawan mutane kuma shine cin zabe. Wadannan dalilai, su ne su ka sa Inyamuri ya kasa samun shugabancin Najeriya a siyasa.
Kuma Obi bai taba nuna kyamatar kiraye-kirayen su Nnamdi Kanu ba, a lokacin mulkinsa mun gani, kashi-kashi yadda ya rika koro Yan Arewa, aka tashi kasuwanninsu guda uku, aka hallaka wasu. Obi bai taba Allah wadai da satar Yara daga Arewa ana kaiwa yankinsu a canza musu al’ada, yare da addini ba. Kuma Kwankwaso ya taba yiwa Obi korafin yadda yake koro Yan Arewa daga jiharsa, hatta ma sai da ya kai shi kara kotu sakamakon haka.
A zaɓen 2027 babu wani abinda ya canza daga wannan tsarin na Inyamuri, obedients ko Obi. Shi ya sa na ke da yakinin ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba cewar Obi ba zai iya cin zabe a 2027 ba. A rubuta a ajiye.
Malam Ali manazarci ne a Kano
