Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina
Gwamnan Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya sanar da cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bada izinin ɗaukar jami’an tsaro da za su kula da tsaron dazuka su 1000 a jihar Katsina.
Dikko ya sanar da haka ne ga manema labarai Jim kaɗan bayan kammala taro da malaman addini da masu ruwa da tsaki a jihar.
Ya bayyana cewa al’umma da sauran masu ruwa da tsaki na da rawar da za su taka wajen samar da tsaro a jihar.
Malam Dikko Raɗɗa ya ce gwamnatin jihar ta shirya wannan taro ne domin sauraran malaman addini a fahimtar su kan musabbabin yadda matsalar tsaro ya ta’azzara da shawarwarin su ta yadda za a shawo kan lamarin.
“Dalilin shirya wannan taro da malaman addini shine mu sauraresu a fahimtar su me ya kawo taɓarɓarewar tsaro a jihar da kuma bada shawarwari da yadda za a maido da zaman lafiya a jihar,”Inji gwamnan.
Ya bayyana cewa jami’an tsaro kaɗai ba za su iya shawo kan matsalar tsaro ba dole sai al’ummomi sun bada ta su gudunmuwa wajen shawo kan ta’adanci a jihar.
Dikko ya ce bincike ya nuna wasu al’ummomi na taimakawa ‘yan bindigan ta hanyar basu bayanai da samar masu da wasu buƙatar su da zai taimaka masu wajen aikata ta’adanci da sayen dabbobin sata.
“Malamammu akwai rawar da za su taka wajen faɗakar da mutane kan canza ɗabi’unsu da ilmantar da al’umma illar da ke tattarre da aikata laifuka,”Dikko ya ce.
Ya bayyana cewa gwamnati ta ɗauki wasu matakai na daƙile ta’adanci a jihar da suka haɗa da haramta zirga zirgan baburan hawa a ƙananan hukumomin Musawa da Matazu.
Haka juma gwamnati ta hana sana’ar POS a yankin domin daƙile hada hadar kuɗaɗe daga hannun ‘yan ta’adda a yankin.
Haka kuma gwamnati ta hana saye,sayarwa da jigilar man Fetur a jarka a duk faɗin jihar.
Gwamnan ya ce gwamnati bata ɗauki wannan mataki ba sai da ta tuntubi masu ruwa da tsaki a yankunan da abin ya shafa.
Ya sanar da cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da ɗaukan matasa maza da mata su 1000 da za su kare dazukan jihar wanda a cewar sa za su taimakawa sauran jami’an tsaro don tabbatar da tsaro a dazukan.
Raɗɗa ya ce wannan tsaron dazuka da za a ɗauka za su sami cikakken hora da samar masu da kayan aiki na kare dazukan.
