Saƙon da Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar a ranar Dimokuraɗiyya ga matasan Nujeriya ya cancanci zurfin tunani. Lokacin da ya buƙace su da su “ginu a nan, su ƙirƙira a nan, su yi aiki a nan, kuma su kaɗa wuri’a a nan,” ya tabo ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta a yau: ƙara yawaitar ficewar matasa masu ilimi, kuɗi da ƙwarewa zuwa ƙasashen waje domin neman ingantacciyar rayuwa.
Furucinsa na cewa “Nijeriya ita ce gidanku kuma makomarku” ya kasance kira ne na kishin ƙasa da kuma ƙalubale ga matasa. Kusan dukkan ƙasashen da suka ci gaba sun samu wannan matsayi ne saboda ’yan ƙasarsu sun zaɓi zama domin gina cibiyoyi, samar da mafita ga matsaloli da kuma ɗora ƙasashensu a kan turbar ci gaba maimakon guduwa lokacin da aka shiga ƙunci.
Babu shakka matasan Nijeriya na da baiwa da hazaƙa mai tarin yawa. A fannoni kamar fasaha, kiwon lafiya, injiniyanci, nishaɗi, wasanni, kasuwanci da masana’antun ƙirƙire-ƙirƙire, matasan Nujeriya na ci gaba da yin fice a duniya. ƙwarewarsu, juriyarsu da basirarsu sun sa suke samun karɓuwa a duk inda suka je. Duk da haka, da yawa daga cikinsu na ƙara ganin makomarsu a wajen Nijeriya.
Abin da aka fi sani da “tserewa” ya zama wani babban al’amari a rayuwar Nijeriya ta wannan zamani. Dubban matasa ƙwararru na barin ƙasar duk shekara zuwa Turai, Amurka, Kanada, Afirka ta Kudu, Ostiraliya da sauran ƙasashe domin neman damar aiki, tsaro, ingantaccen ilimi da rayuwa mai kyau. Idan aka yi la’akari da matsalolin rashin aikin yi, hauhawar farashi, rashin tsaro, ƙarancin ababen more rayuwa da rashin tabbas a tattalin arziki, ba abin mamaki ba ne yadda suke jin takaici.
Sai dai kuma, hijira ba kullum take zama alheri kamar yadda wasu ke zato ba. ƙwarewar ’yan Nujeriya da ke zaune a ƙasashen waje ta nuna cewa akwai ƙalubale masu yawa. A Afirka ta Kudu, hare-haren baƙin haure sun yi sanadin mutuwa, raunuka da lalata dukiyoyin ’yan Afirka, ciki har da ’yan Nijeriya. Haka kuma, dangantakar Nijeriya da Ghana ta taɓa fuskantar tangarɗa saboda rikice-rikicen da suka shafi ’yan kasuwa da baƙin haure ’yan Nijeriya.
A Habasha ma akwai darasi mai muhimmanci. Kwanan nan Nijeriya da Habasha sun rattaba hannu kan yarjejeniyar mayar da fursunoni gida, wadda za ta bai wa sama da ’yan Nijeriya 100 damar dawowa daga gidajen yari na Habasha. Wasu daga cikinsu sun shafe shekaru a kurkuku, yayin da wasu ma suka mutu kafin cimma yarjejeniyar. Wannan ya sake nuna irin farashin da wasu ke biya wajen neman rayuwa a ƙasashen waje.
Haka kuma a Turai da Arewacin Amurka, wasu baƙin haure na fuskantar wariya, kaɗaici, matsalolin samun aiki da kuma tsauraran dokokin shige da fice. Duk waɗannan misalai na nuna cewa babu wata ƙasa da za ta iya maye gurbin Nijeriya mai ci gaba da aiki yadda ya kamata.
Ko da yake hijira haƙƙi ne na kowane mutum, Nujeriya ba za ta iya jure rasa mafi yawan haziƙan ’ya’yanta ba. ƙasar da kullum take fitar da mafi ƙwazonta zuwa ƙetare na iya raunana damar ci gabanta. Wannan ne ya sa kiran Shugaba Tinubu ya cancanci goyon baya. Amma kishin ƙasa ba ya ɗorewa da kalamai kaɗai. Ba za a iya sa ran matasa su zauna a Nijeriya saboda an gaya musu su zauna ba. Dole ne a samar musu da dalilan da za su sa su yi hakan.
A nan ne gwamnati ke da babban aiki. Dole ne ta tabbatar da cewa gyare-gyaren tattalin arziki sun haifar da ayyukan yi, sauƙaƙa samun rance, tallafa wa harkokin kasuwanci da samar da yanayin da zai ƙarfafa masu zuba jari. Haka kuma, ya zama wajibi a saka hannun jari a ilimi domin samar da ƙwararrun da za su iya fafatawa a kasuwar duniya.
Matsalolin wutar lantarki, sufuri da hanyoyin sadarwa na zamani na buƙatar kulawa cikin gaggawa. Haka kuma, babu wata al’umma da za ta iya riƙe mafi kyawun ’ya’yanta idan mutane na rayuwa cikin tsoro. Matasa masu sana’o’i da masu ƙirƙire-ƙirƙire suna buƙatar muhalli mai kwanciyar hankali domin cimma burinsu.
Gwamnati ta kuma kamata ta ƙara tallafa wa cibiyoyin ƙirƙire-ƙirƙire, cibiyoyin koyon sana’o’i, masana’antun fasaha, harkokin nishaɗi da kuma noma na zamani. Ya kamata a daina kallon yawan matasan Nijeriya a matsayin matsala, a maimakon haka a gan su a matsayin mafi girman kadarar dabarun ci gaban ƙasa.
A gefe guda kuma, matasa dole su fahimci cewa gina ƙasa nauyi ne na kowa. Shiga harkokin dimokuraɗiyya, ƙirƙira, kasuwanci da bayar da gudunmawa ta hanyar da ta dace su ne ginshiƙan canjin da ake nema.
Shugaba Tinubu ya yi gaskiya lokacin da ya ce Nijeriya na buƙatar matasanta. Babu wata ƙasa da za ta iya ba wasu amanar makomarta. Injiniyoyin da za su gina ababen more rayuwa, likitocin da za su inganta kiwon lafiya, masu shirya manhajoji da za su bunƙasa tattalin arzikin zamani da shugabannin da za su ƙarfafa dimokuraɗiyya dole ne su fito daga cikin al’ummar ƙasar.
Sai dai kuma gwamnati na da alhakin tabbatar da cewa zama a Nijeriya ba sadaukarwa ba ne, illa wata dama ce ta samun nasara da cikar buri. Saƙon a bayyane yake: Nijeriya na buƙatar matasanta, kuma matasan suna buƙatar Nijeriya mai aiki. Idan waɗannan abubuwa biyu suka haɗu, burin samun Nijeriya mai wadata, kwanciyar hankali da ƙarfin gasa a duniya zai zama gaskiya.
