Yadda tsadar aure ke ƙara yawaitar zinace-zinace cikin al’umma – Adamu Nuhu

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Wani matashin malamin addinin Musulunci, Malam Adamu Nuhu Argungu, ya bayyana damuwarsa kan yadda zina ke kara yaduwa a cikin al’umma, yana mai danganta lamarin da tsadar aure da kuma wasu al’adu da suka sanya yin aure ya zama mai wahala ga matasa.

Malamin ya bayyana hakan ne yayin wata laccar aure da ya gabatar a garin Argungu a makon da ya gabata.

A cewarsa, a halin yanzu mutum na iya mallakar Naira 500,000 amma har yanzu kudin ba su isa ya gudanar da aure cikin sauki ba saboda yawan kudaden al’ada, lefe da sauran shirye-shiryen biki da iyalai ke dorawa masu neman aure.

Ya ce abin takaici ne yadda aure, wanda addinin Musulunci ya saukaka, ya zama mai wahala, yayin da zina, wadda Allah Ya haramta, ta zama mai saukin aikatawa.

“Yau da Naira dubu biyar zuwa dubu goma kacal, ko ma da kalaman yaudara da alƙawuran ƙarya, wasu na iya jawo mata zuwa aikata abin da bai dace ba. Wannan wani babban kalubale ne ga tarbiyya da zaman lafiyar al’umma,” inji shi.

Malam Adamu ya bayyana cewa matsalar tana bukatar a duba ta ta fannoni daban-daban, musamman daga bangaren iyaye, matasa da kuma al’umma baki ɗaya.

Ya yi kira ga iyaye da su rage nauyin bukatun da ake dorawa masu neman aure, yana mai cewa yawan kuɗaɗen da ake buƙata da kuma gasar bukukuwa na hana matasa da dama shiga rayuwar aure cikin sauƙi.

A cewarsa, irin wannan matsin lamba na iya sa wasu ’yan mata su daɗe ba tare da aure ba, lamarin da kan buɗe ƙofar faɗawa cikin matsalolin da ba a so.

Har ila yau, malamin ya yi kira ga ’yan mata da su mutunta kansu tare da kare kimarsu da mutuncinsu.

Ya ce: “Ya kamata kowace budurwa ta fahimci cewa mutuncinta ya fi duk wani abin duniya daraja. Duk wanda ba zai iya zuwa wajen iyayenta domin neman aurenta ta hanyar da ta dace ba, ya kamata ta yi taka-tsantsan da manufarsa.”

Malam Adamu ya kuma yi kira ga samari da su ji tsoron Allah wajen mu’amalarsu da mata, yana mai jaddada muhimmancin neman halal maimakon faɗawa cikin abubuwan da addini ya haramta.

Ya ce idan aka yi amfani da kuɗaɗen da ake kashewa wajen neman biyan buƙatu ta haramtacciyar hanya wajen shirya aure, hakan zai taimaka wajen gina iyalai masu ɗorewa da kuma samar da zaman lafiya a cikin al’umma.

A ƙarshe, malamin ya bukaci al’umma da su koma ga koyarwar addini da kyawawan al’adu da suka ginu a kan sauƙaƙa aure da kare tarbiyya, domin magance matsalolin da ke fuskantar matasa a wannan zamani.

By ukarofi