An fara raba muhimman kayan zaɓe gabanin zaɓen Gwamnan Ekiti

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar da fara raba kayan zaɓe masu muhimmanci daga Babban Bankin Najeriya (CBN) domin shirye-shiryen zaɓen gwamnan jihar Ekiti da wasu zaɓukan cike gurbi na majalisun tarayya da za a gudanar ranar Asabar, 20 ga Yuni, 2026.

Hukumar ta kuma bayyana cewa adadin masu rajistar zaɓe a jihar Ekiti ya ƙaru daga mutum 987,647 a shekarar 2023 zuwa 1,059,360 a shekarar 2026.

A cikin wata sanarwa da shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Ilimantar da Masu Zaɓe na INEC, Mohammed Haruna, ya fitar, ya ce adadin waɗanda suka karɓi katin zaɓensu na dindindin (PɓC) ya ƙaru daga 958,052 a shekarar 2023 zuwa 1,028,929 a shekarar 2026.

Sanarwar ta ce hakan na nufin kashi 97 cikin 100 na katunan da aka fitar an riga an karɓe su, wanda ya kai kashi 97.1 cikin 100 na jimillar masu rajistar zaɓe a jihar.

INEC ta ce ta kammala aikin rabon katunan zaɓe cikin nasara kafin zaɓen da za a gudanar ranar Asabar.

A baya dai an tsara kammala rabon katunan ne a ranar 11 ga Yuni, amma bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a Ado-Ekiti, an tsawaita wa’adin zuwa ranar 14 ga Yuni, 2026.

Hukumar ta kuma bayyana cewa, bisa tanadin sashe na 18(1) na Dokar Zaɓe ta 2026, ta karɓi buƙatu 14,406 daga masu neman maye gurbin katin zaɓensu da ya ɓace, ya lalace ko ya salwanta.

A cewar INEC, an buga dukkan katunan maye gurbin da aka nema, kuma mafi yawansu an riga an karɓe su.

Sai dai hukumar ta bayyana cewa ba za a iya amfani da tsarin sauke kwafin katin zaɓe ta yanar gizo ba a wannan zaɓe, saboda har yanzu ba a kammala samar da fasahar da ake buƙata domin aiwatar da tsarin ba.

INEC ta ce ana sa ran fara amfani da wannan fasaha a zaɓen gwamnan jihar Osun da za a gudanar a watan Agustan 2026, da kuma babban zaɓen shekarar 2027.

Hukumar ta tabbatar wa al’umma cewa dukkan shirye-shiryen gudanar da sahihin zaɓe cikin lumana da adalci suna tafiya yadda ya kamata, tare da kira ga masu zaɓe da su fito su yi amfani da haƙƙinsu na zaɓe cikin lumana.

By ukarofi

Leave a Reply