Fraministan Birtaniya, Keir Starmer ya yi murabus daga muƙaminsa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya sanar da yin murabus ɗansa daga muƙaminsa yayin da ake raɗe-raɗin shirinsa na sauka daga muƙamin tare da jaddada goyon bayan ga magajinsa.

A cikin wani jawabinsa mai cike da ƙawa-zuci, Starmer ya bayyana cewa ya saurari ra’ayin jam’iyyarsa ta Labour Party akan ko har yanzu shi ne ya fi dacewa ya jagorance ta zuwa babban zaɓe na gaba.

Ya ce, ya amince da sakamakon wannan ra’ayi cikin mutunci da kyakkyawar niyya, yana mai cewa ya samu amsar da jam’iyyar ta bayar game da makomarsa a shugabanci.

Starmer mai shekaru 63,wanda kuma tsohon lauya ne ya fuskanci matsaloli daga masu zaɓe akan rashin kyawun salon tsare-tsare da wasu zarge-zarge.

A shekarar 2024 ne Starmer ya lashe zaɓen mafiya rinjaye a majalisar ƙasar ga Labour tun 1997 bayan jagoranci gwamnatin jam’iyyar Conservative na tsawon shekaru 14.

By Babaji