Mutane biyar sun mutu a rikicin manoma da makiyaya a garin Gulma

Spread the love

Daga JAMIL GULMA

Yanzu haka dai ana zaman ɗar-ɗar tsakanin mutanen garin Gulma da ke ƙaramar hukumar Argungu da kuma makiyaya Fulanin da ke zaune a kewaye da su bayan mutuwar a ƙalla mutane biyar da rikicin manoma da Fulani ya rutsa da su ranar Litinin ɗin nan.
Wani mazauni garin Gulma Malam Hussaini ya bayyanawa waƙilin jaridar Blueprint Manhaja da cewa
Kwanakin baya ne shanun fulani suka shiga gonar da wani manomi Alhaji Aminu mai kimanin shekaru 35 ke noman shinkafa, a ƙoƙarin sa na korar shanun ya karya ƙafar shanuwa ɗaya.
Tun daga wannan lokacin shi kuma bafillatanin ya ƙullace shi, sai yau Litinin bayan Sallar Azahar Alhaji Aminu ya tafi gonar suka haɗu da wannan Bafillacen inda ya tsokane shi da wannan maganar daga nan sai suka fara faɗa, bayan Alhaji Aminu ya kada bafillatanin shi kuma ya zaro wuƙa ya soke shi a ciki wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sa.
Bayan labari ya iso cikin gari sai matasa suka fito da makamai suka far wa fulani tun a cikin gari.
Kawo yanzu dai an kashe fulani huɗu kuma an ƙona gawar Bafillacen da ya yi kisan ita kuma gawar Alhaji Aminu tuni an yi masa jana’iza.

PPRO ASP Bashir ya bayyana cewa tuni jami’an ƴan sanda sun isa garin Gulma kuma sun kama waɗansu mutane daga cikin gari da kuma Fulani don binciken musabbabin wannan matsalar.
An kuma girke jami’an Sojoji a garin don dawowa da zaman lafiya.

Waƙilin blueprint Manhaja ya kira shugaban ƙaramar hukumar Argungu Honarabul Aliyu Sani Gulma bai ɗauki waya ba kuma bai amsa saƙon kar-ta-kwana har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

By ukarofi

Leave a Reply