
A yau Talata Shugaba Bola Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa ƙudirin gyaran kundin tsarin mulki domin bayar da damar sanya dokar kafa rundunar ‘yan sandan jihohi a faɗin Nijeriya.
Ƙudirin na neman yin gyare-gyare ne ga wasu sassan kundin tsarin mulkin shekarar 1999 domin samar da sahihin tsarin doka da zai bai wa jihohi damar kafa rundunonin ’yan sandansu.
Matakin ya biyo bayan kiraye-kirayen da shugaban ƙasar ya dinga yi na a yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima domin bai wa jihohi damar taka rawar gani wajen samar da tsaro a yankunansu.
A watan Fabrairun wannan shekara, Tinubu ya buƙaci Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta yi gyaran kundin tsarin mulki domin ba da damar kafa ’yan sandan jihohi, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen yaƙi da ta’addanci, fashi da makami da kuma ayyukan ’yan bindiga.
A jawabin da ya gabatar ranar Dimukraɗiyya a farkon watan nan, shugaban ƙasar ya jaddada cewa gwamnati za ta cigaba da ɗaukar mataki mai tsauri akan ’yan ta’adda, ’yan bindiga da masu ɗaukar nauyinsu, yana mai cewa ba za a nuna sassauci ga maƙiyan ƙasa ba yayin da ake ƙoƙarin samar da ci-gaba.
Ana sa ran Majalisar Dattawa za ta gudanar da zama na musamman domin nazari da kuma ɗaukar mataki kan kudirin, wanda ake ganin na daga cikin manyan sauye-sauyen tsaro a tarihin Nijeriya.
