Majalisar Dokokin Katsina ta yi kira da a cigaba da fatattakar ‘yan bindiga

Spread the love


Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Majalisar dokokin jihar Katsina ta yaba da ƙoƙarin Gwamnati na kawo ƙarshen matsalar tsaro tare da yin kira da a ƙara ƙaimi wajen dawo da zaman lafiya jihar.

A zaman wanda ya gudana ƙarƙashin jagorancin kakakin majalisar dokokin Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura, majalisar ta maida hankali kan matsalolin tsaro da suka shafi wasu yankunan jihar.

An gabatar da ƙudurin haɗin gwiwa da shugaban masu tsawatarwa na majalisar, Hon. Ibrahim Umar Dikko, mai wakiltar mazaɓar Matazu kuma bulaliya na majalisar ya jagoranta, tare da mataimakin shugaban masu tsawatarwa, Hon. Salisu Hamza Rimaye, mai wakiltar mazabar Kankia, da Hon. Lawal H. Yaro mai wakiltar mazaɓar Musawa, da kuma Hon. Lawal Isa Kuraye mai wakiltar mazabar Charanchi.

‘Yan majalisar sun bayyana damuwarsu kan hare-haren da suka addabi wasu sassan ƙananan hukumomin Charanchi, Kankia, Matazu da Musawa, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren.

Yan majalisar sun yabawa gwamnatin jihar da hukumomin tsaro bisa matakan gaggawa da suka ɗauka domin daƙile matsalar da kuma dawo da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.

Bayan gabatar da ƙudurin da muhawara daga mambobin majalisar, majalisar ta amince da ƙudurin tare da yaba wa gwamnatin jihar da jami’an tsaro kan ƙoƙarin da suke yi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Majalisar ta kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su ci gaba da ƙara ƙaimi wajen tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a dukkan sassan jihar, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin al’umma da jami’an tsaro domin samun nasarar yaƙi da masu tayar da zaune tsaye.

By ukarofi

Leave a Reply