
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kamfanin Shirya Finafinai na Abnur Entertainment ya nesanta kansa da kalaman jaruma Nafisa Abdullahi ta cikin fim ɗin Ƙaddara, waɗanda suka tayar da ƙura a kafafen sada zumunta a kwanan nan.
A wata sanarwa da Abnur ya fitar a ranar Talata, 23 ga Yuni, 2026, ya ce “Ƙaddara” da ɗaukacin waɗanda suka shirya ba su da wata alaƙa da kalaman jarumar da suka shafi batun aure.
A cewarsa, Nafisa Abdullahi ra’ayin ƙashin kanta ta bayyana don haka ba ya wakiltar fim ɗin ko sauran waɗanda aka yi shi da su ko wani ɓangarensa.
Ya bayyana cewa: “Mu a matsayinmu na masu shirya finafinai, muna mutunta darajar aure da muhimmancinsa acikin addini da al’adunmu. Haka kuma muna Alla-wadai da dukkan wani furuci da zai iya rage martabar aure ko ya janyo ruɗani a tsakanin al’umma.”
A ƙarshe, Abnur Entertainment ya yi magiya ga masoya da masu a kallon fim ɗin Ƙaddara da su riƙa bambanta tsakanin ra’ayin mutum da kuma aikin da ake gabatarwa musamman ga fim ɗin, wanda ana yin sa ne domin nishaɗantarwa da faɗakarwa don haka ba shi da alaƙa da wannan batu.
A kwanan nan ne aka ga jarumar a wani shiri tana furta wasu kalamai akan lamarin aure da wasu ke ganin su a matsayin karan-tsaye ga addini da kuma al’ada.
