Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
A cigaba da shirye-shiryen ƙaddamar da littafin “Mu San Magabata”, wanda Injiniya Kabiru Ahmad Ƙwalli ya rubuta.
Littafin wanda ya ƙunshi tarihi da muhimmiyar rawa da waɗannan mutane suka taka wajen ci gaban jihar a fannoni daban-daban.
A yayin zaman ƴan kwamitin da ya gudana a Mustibrah Polytechnic da ke Kano, kwamitin ya sanya ranar Asabar 27/ 6/ 2026 a matsayin ranar ƙaddamarwa a ɗakin taro na Farfesa Hafizu Abubakar dake Jamiar North West da ke cikin birnin Kano.
Ana sa ran Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf zai halacci taron yayin da mai martaba Sarkin Kano Mal. Muhammadu Sanusi Lamido Sanusi zai kasance uban taro.
Ƙwalli ya ce manufarsa ita ce cike giɓi wajen rubuce rubucen tarihi, ganin cewa yawancin manyan mutanen Kano ba su da cikakkun kundin tarihin rayuwarsu, duk da gagarumar gudummawar da suka bayar.
Littafin ya yi duba ne kan shugabanni, malamai, ‘yan kasuwa da jajirtattun masu hidima ga al’umma da suka yi fice a tarihi. Fitattun sunayen da suka fito a littafin sun haɗa da:
Madakin Kano Shehu Ahmad, Alƙalin Kano Umaru, Sheikh Sani Auwalu Darma, Alhaji Uba Ringim, Alhaji Imam Wali, Alhaji Ado Dandolo,
Malam Nura Alƙali, Malam Adamu Aminu.
Sauran sun haɗa da: Kansila Malam Ahmadu Rufa’i Daura, Alhaji Barau Maiwake, Alhaji Baballe Ila, Alhaji Baffa Yola, Alhaji Muhammadu ‘Yankwashi Kazaure, Alhaji Mahe Bashir Wali, Alhaji Salisu Sambajo da Alƙali Husaini Sufi da dai sauran sanannun jaruman al’umma har zuwa mutum 24.
Kwamitin ƙarƙashin jagorancin Farfesa Bashir Yusuf, tare da Alhaji Ibrahim Aminu Dan’Iya a matsayin mataimaki.
Sanata Barau I. Maliya CRF mataimakin shugaban Majalisar Dattawa ne zai zama baƙo na musamman, yayin da Gen. Salihi Magashi zai zama babban mai ƙaddamarwa, yayin da manyan mutane daga sassa daban-daban na jihar Kano da wajen Kano za su take masa baya.
Kazalika, kwamitin ya ce Farfesa Abdullah Uba Adamu shi ne zai zama baƙo mai jawabi sai Farfesa Ibrahim G. Satatima zai kasance mai bitar littafi.
Kwamitin na fatan alumma za su halarta duka dai don ganin wannan ƙaddamarwar ta samu nasara, wanda daga nan sai littafin ya shiga hannun al’umma.
