
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya amince da kafa kwamiti na musamman domin gudanar da bincike akan ababen da suka yi sanadiyyar mutuwar wata ɗaliba ta makarantar St. Louis College da ke Kano.
Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya sanar da haka a ranar Alhamis a Kano, cikin wata takarda.
Ya ce, Alhaji Ali Makoɗa, Kwamishinan Ilimin jihar ne zai jagoranci kwamitin, wanda ya ƙunshi masu ruwa da tsaki a fanin ilimi, shari’a, makarantun kuɗi da kuma wakilan makarantar da abin ya shafa.
Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Aminu Hussain, Hamza Dantani, Abubakar Umar, Sunusi Dawaki-Tofa, Ahmed Zuabairu, Hafsat Adhama da kuma Binta Mukhtar.
A cewar kakakin, nauyin kwamitin ya haɗa da nazari akan ababen da suka sabbaba mutuwar ɗalibar, rahotannin lafiya, rahotannin hukuma da binciken kewayen makarantar da dai sauransu.
A wani ɓangare kuwa, rundunar ‘yan sandan jihar ƙarƙashin jagorancin Kwamishina Ibrahim Bakori, ta samar da kwamiti na musamman domin binciken musabbabin faruwar mutuwar ɗalibar.
Binciken rundunar na zuwa ne bayan wani ƙorafi da mahaifiyar ɗalibar, Nusaiba Rabi’u ta shigar a kotu akan rasuwar ‘yarta mai suna Maimuna Sani Salisu da ke aji 2 a Ƙaramar Sakandare ta kwana a St. Louis, Kano.
