Daga MU’AZU HARDAWA a Bauchi
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta yi nasarar ceto wasu yara mata biyu masu shekaru 13 da aka sace daga Jihar Taraba, tare da kama wasu matasa biyu da ake zargi da hannu wajen aikata laifin a ƙaramar Hukumar Kirfi ta jihar.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, SP Nafiu Habib, ya fitar, ya bayyana cewa an ceto yaran ne bayan wani mutum mai shekaru 57 daga ƙauyen Fangari da ke ƙaramar Hukumar Bali a Jihar Taraba ya kai rahoton ɓacewarsu ga jami’an tsaro a ranar 10 ga Maris, 2026.
Mahafin yaran ya bayyana cewa diyarsa, Aisha mai shekaru 13, tare da kawarta Zainab, ita ma mai shekaru 13, sun ɓace daga gida ba tare da an san inda suka nufa ba, kuma duk ƙoƙarin gano su bai yi nasara ba.
Bayan samun rahoton, jami’an ’yan sanda suka fara bincike tare da tattara bayanan sirri, lamarin da ya kai ga gano yaran a garin Bara da ke ƙaramar Hukumar Kirfi a Jihar Bauchi.
Binciken ya nuna cewa wasu matasa biyu, Auwal Muhammad da Abdulgaffar Musa, duk masu shekaru 20 kuma mazauna Unguwar Zangoma a Bara, sun haɗa baki wajen ɗauko yaran daga Taraba zuwa Bauchi ba tare da amincewar iyayensu ba.
Rundunar ta ce an kama waɗanda ake zargin, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen haɗa yaran da iyayensu. Haka kuma an miƙa lamarin ga Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) domin zurfafa bincike da kuma gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya jaddada cewa rundunar ba za ta lamunci sace yara ko duk wani nau’in cin zarafi a kan yara ba. Ya kuma yi kira ga iyaye da masu kula da yara da su ƙara sanya ido a kan ’ya’yansu tare da kai rahoton duk wani abin da ya tayar musu da hankali ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.
