ACF ta ƙaddamar da kwamitin asusun waƙafi domin bunƙasa ilimi da ci gaban Arewa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa, wato Arewa Consultative Forum (ACF), ta ƙaddamar da Kwamitin Asusun Waƙafi da nufin inganta ilimi, bunƙasa tattalin arziki da kuma aiwatar da ayyukan ci gaban al’umma a faɗin Arewacin Nijeriya.

An naɗa tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Muhammad Dikko Abubakar, a matsayin shugaban kwamitin, inda aka ɗora masa alhakin jagorantar aiwatar da manufofi da tabbatar da cimma burin da aka kafa asusun domin su.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da kwamitin, Shugaban ACF kuma Wazirin Dutse, Alhaji Bashir Dalhatu, ya yaba wa mambobin ƙungiyar bisa sadaukarwa, goyon baya da kuma jajircewarsu wajen ci gaban ƙungiyar.

Ya bayyana cewa kafa Asusun waƙafiwani muhimmin mataki ne na faɗaɗa damar ilimi, tallafa wa shirye-shiryen ci gaban al’umma da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa a yankin Arewa.

Alhaji Bashir Dalhatu ya bayyana cewa ACF ta ƙaddamar da Asusun waƙafi na Naira biliyan 100 a lokacin bikin cika shekaru 25 da kafuwar ƙungiyar. Ya ce an samu alkawuran bayar da gudunmawar da suka kai Naira biliyan 7.8, amma zuwa yanzu an biya Naira biliyan 3.9 kacal, waɗanda ke cikin asusun ACF a bankin Jaiz.

Ya tabbatar wa mambobi da masu ruwa da tsaki cewa kuɗaɗen asusun suna cikin tsaro, tare da ƙarfafa sabon kwamitin da ya fara aiki wajen gudanar da ayyukan jin ƙai da ci gaban al’umma a dukkan sassan Arewa.

Haka kuma ya buƙaci waɗanda suka yi alƙawarin bayar da gudunmawa da su cika alƙawarinsu domin ƙara ƙarfin asusun.

“Ayyukan alherin da za mu gudanar da kuɗaɗen da muke da su yanzu za su jawo ƙarin masu bayar da tallafi a nan gaba,” inji shi.

Shugaban ACF ya ƙara da cewa ƙungiyar za ta ci gaba da haɗa kai da masu ruwa da tsaki, abokan hulɗar ci gaba da shugabannin al’umma domin inganta zaman lafiya, haɗin kai, shugabanci nagari da ci gaban ƙasa.

Ya ce gudunmawar da mambobin ACF ke bayarwa ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen gina ƙasa da kuma dawo da kyawawan ɗabi’u da za su samar da zaman lafiya, ci gaba da wadata ga al’ummar Nijeriya baki ɗaya.

Ana sa ran sabon Asusun waƙafin zai kasance wata sahihiyar hanya mai gaskiya da riƙon amana wajen tattara kuɗaɗe domin tallafa wa shirye-shiryen ilimi, ƙarfafa matasa, bunƙasa shugabanci da sauran ayyukan da za su inganta rayuwar al’ummomin Arewacin Nijeriya.

ƙaddamar da kwamitin na daga cikin ƙoƙarin ACF na samar da ingantattun hanyoyin ci gaba da zuba jari a fannin bunƙasa albarkatun ɗan Adam domin tabbatar da kyakkyawar makoma ga yankin Arewa da Nijeriya baki ɗaya.

ACF ta jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki tare da kowa domin gina Nijeriya mai ƙarfi, haɗin kai da wadata ga kowa.

By ukarofi