Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya aike wa majalisar dattawa da ƙudirin gyaran kundin tsarin mulki domin kafa rundunar ’yan sandan jihohi a faɗin ƙasar nan.
ƙudirin na neman yin gyare-gyare ga wasu sassan kundin tsarin mulkin shekarar 1999 domin samar da sahihin tsarin doka da zai bai wa jihohi damar kafa rundunonin ’yan sandansu.
Matakin ya biyo bayan kiraye-kirayen da shugaban ƙasar ya dinga yi na a yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima domin bai wa jihohi damar taka rawar gani wajen samar da tsaro a yankunansu.
A watan Fabrairun wannan shekara, Tinubu ya buƙaci Majalisar Dokoki ta ƙasa ta yi gyaran kundin tsarin mulki domin ba da damar kafa ’yan sandan jihohi, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen yaƙi da ta’addanci, fashi da makami da kuma ayyukan ’yan bindiga.
A jawabin da ya gabatar ranar dimokuraɗiyya a farkon watan nan, shugaban ƙasar ya jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da ɗaukar mataki mai tsauri kan ’yan ta’adda, ’yan bindiga da masu ɗaukar nauyinsu, yana mai cewa ba za a nuna sassauci ga maƙiyan ƙasa ba.
Tinubu ya kuma bayyana cewa sama da ’yan ta’adda 13,000 ne aka kashe cikin shekara guda da ta gabata, tare da cewa yawan mace-macen da ke da alaƙa da ta’addanci ya ragu idan aka kwatanta da shekarun baya.
Sai dai ya amince cewa ci gaba da tsare ɗaliban da aka sace a jihohin Oyo da Borno na nuna cewa har yanzu Nijeriya na fuskantar manyan ƙalubalen tsaro.
A watannin baya-bayan nan, batun kafa ’yan sandan jihohi ya samu karɓuwa, yayin da majalisun dokoki na ƙasa ke ci gaba da nazarin gyaran kundin tsarin mulki domin bai wa jihohi ƙarin iko kan harkokin tsaro.
Ana kuma sa ran Majalisar Dattawa za ta gudanar da zama na musamman domin nazari da kuma ɗaukar mataki kan kudirin, wanda ake ganin na daga cikin manyan sauye-sauyen tsaro a tarihin dimokuraɗiyyar Nijeriya.
