Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo ta bayyana cewa rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa an ceto wasu mutane biyu da aka sace a yankin Igbope ƙarya ce, marar tushe kuma mai yaudarar jama’a.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ƙarƙashin taken “Martanin Hukuma”, ta bayyana cewa bidiyon da ake yaɗawa da ke nuna wai an ceto waɗanda aka sace ba shi da inganci kuma ba a tabbatar da sahihancinsa ba.
Sanarwar ta ce mutanen da aka sace, wato Misis Kuburat Omowumi da ɗanta, an yi garkuwa da su ne a ranar 16 ga Yuni, 2026, kuma har yanzu jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da bincike da ayyukan ceto domin tabbatar da an kuɓutar da su cikin koshin lafiya.
Rundunar ta jaddada cewa tun bayan da aka kai rahoton sace su, ta ƙara kaimi wajen gudanar da ayyukan tsaro da tattara bayanan sirri tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki domin ceto waɗanda aka sace tare da kamo masu hannu a laifin.
Ta yi gargaɗin cewa yaɗa bayanan da ba a tantance ba a irin wannan lokaci na iya haifar da ruɗani, gina ƙagaggun labarai da kuma kawo cikas ga ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi na ceto mutanen.
Saboda haka, rundunar ta buƙaci jama’a da su dogara ne kawai da bayanan da hukumomin tsaro suka fitar a hukumance, tare da tabbatar da sahihancin duk wani bayani kafin yaɗa shi.
Haka kuma, ta yi kira ga duk wanda ke da sahihan bayanai da za su taimaka wajen ceto waɗanda aka sace da kuma kamo masu laifi da ya miƙa su ga jami’an tsaro domin taimakawa wajen nasarar ayyukan da ake gudanarwa.
