
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙasashen Ingila, Portugal, Ghana, Misra da Paraguay sun yi nasarar tsallakewa zuwa zagayen ‘yan 32 a gasar Kofin Duniya da ke cigaba da gudana a Nahiyar Amurka.
Duk cewa, Ingila, Portugal Ghana da Misra suna da sauran wasa guda-guda a zangon rukunin-rukuni, sakamakon wasannin da aka buga a yanzu sun nuna cewa sun riga sun yi nasarar tsallakewa zuwa zagaye na gaba a gasar, wanda aka faɗaɗa adadin ƙasashensa zuwa 48.
Paraguay ce ƙasa ɗaya daga cikin biyar ɗin da ta kammala buga wasanninta uku na rukunin, inda ta samu maki huɗu da suka ba ta damar zuwa zagayen.
