Ya rayu tsawon kwana 100 da zuciyar ƙarfe

Spread the love

Wani mutum a ƙasar Ostiraliya ya kafa tarihi bayan ya rayu sama da kwanaki 100 da wata cikakkiyar zuciyar ƙarfe da aka dasa masa yayin da yake jiran a samo masa zuciyar da za a yi dashen ta.

Likitoci sun bayyana cewa zuciyar ta amfani da na’ura ce ta zamani wadda ke aikin bugun zuciya kamar yadda zuciyar ɗan Adam ke yi. Wannan ya ba mutumin damar rayuwa da gudanar da wasu ayyuka na yau da kullum duk da cewa zuciyarsa ta asali ta daina aiki.

Bayan shafe fiye da watanni uku da wannan zuciyar ta wucin gadi, daga ƙarshe an samu zuciyar da ta dace da shi, inda aka yi masa dashen cikin nasara.

Masana sun ce wannan nasara ta buɗe sabon babi a fannin kula da marasa lafiya masu fama da matsananciyar cutar zuciya, kuma tana iya taimaka wa dubban mutane a nan gaba.

By ukarofi

Leave a Reply