Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) da Hukumar Kula da Rijistar Kamfanoni (CAC) sun fitar da sabbin ƙa’idoji da suka wajabta wa kamfanonin sadarwa samun amincewar hukuma kafin aiwatar da manyan sauye-sauye a tsarin mallakarsu.
Sabuwar dokar ta tanadi cewa duk wani canjin hannun jari da ya kai ko ya wuce kashi 10 cikin 100 a kamfanin da ke da lasisin NCC, dole ne ya samu Takardar Rashin Adawa daga Hukumar Sadarwa ta Nijeriya kafin Hukumar CAC ta amince da rajistar canjin.
A cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa da hukumomin biyu suka fitar a ranar Lahadi, sun bayyana cewa dokar ta fara aiki nan take, lamarin da ke nuna wani sabon mataki na tsaurara sa ido kan harkokin masu zuba jari da kamfanonin sadarwa a ƙasar.
Sanarwar ta ce matakin ya samo asali ne daga sashe na 90 na Dokar Sadarwa ta Nijeriya ta shekarar 2003, da kuma wasu ƙa’idojin kula da gasa da lasisi waɗanda suka bai wa NCC ikon duba da sa ido kan mu’amalolin da suka shafi kamfanonin da ta ba lasisi.
Hukumomin sun kuma bayyana cewa wannan sharadi ba ya tsaya ga sauyin hannun jari guda ɗaya kawai, domin har ma idan an yi jerin sauye-sauye daban-daban da jimillarsu ta kai sama da kashi 10 cikin 100, sai an samu amincewar NCC kafin a yi rajistarsu.
A cewar sanarwar, daga yanzu CAC ba za ta amince da rajistar irin waɗannan sauye-sauyen mallaka ba sai an gabatar da hujjar cewa NCC ta amince da su tun kafin a aiwatar da su.
NCC da CAC sun bayyana cewa manufar wannan mataki ita ce kare tsarin gasa mai adalci a ɓangaren sadarwa tare da hana duk wani canjin mallaka da zai iya haifar da mamaye kasuwa ko karya dokokin gasa.
Sun ce sabuwar dokar za ta ƙara tabbatar da gaskiya da riƙon amana a harkokin kasuwanci, tare da ƙarfafa amincewar masu zuba jari da samar da tabbas ga masu ruwa da tsaki a fannin sadarwa.
Haka kuma, hukumomin sun jaddada cewa ƙarin sa ido kan sauye-sauyen mallaka zai taimaka wajen tabbatar da ɗorewa da zaman lafiyar masana’antar sadarwa, wadda ke taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arzikin zamani na Nijeriya.
A ƙarshe, NCC da CAC sun sake nanata aniyarsu ta ci gaba da aiki tare domin tabbatar da bin doka, inganta gasa mai adalci da kuma tallafa wa ci gaban ɓangaren sadarwa cikin tsari mai ɗorewa.
