Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Masu ababen hawa da dama a Babban Birnin Tarayya Abuja, sun nuna damuwa kan yadda farashin fetur ke ci gaba da kasancewa mai tsada duk da raguwar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.
Masu motocin sun bayyana cewa har yanzu gidajen mai da dama a faɗin Abuja ba su daidaita farashin su yadda ya kamata ba, duk kuwa da sauyin da aka samu a kasuwar makamashi ta duniya.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa farashin gangar ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya ragu daga dala 150 zuwa kasa da dala 80. Ana danganta wannan sauyi da sassautuwar rikicin da ya dabaibaye Amurka da Iran a baya-bayan nan.
Bayan faɗuwar farashin ɗanyen mai zuwa kasa da dala 80 kan kowace ganga, Matatar Dangote ta rage farashin fetur da take sayarwa ga dillalai da naira 75 kan kowace lita.
Binciken da NAN ta gudanar ya nuna cewa wasu gidajen mai kamar MRS sun rage farashin su zuwa tsakanin naira 1,241 da naira 1,261 kan kowace lita, yayin da wasu gidajen mai ke ci gaba da sayar da fetur tsakanin naira 1,335 da naira 1,360 kan kowace lita.
A nata ɓangaren, ƙungiyar Masu Gidajen Sayar da Man Fetur ta Nijeriya (PETROAN) ta buƙaci masu shigo da fetur daga ƙasashen waje da su yi la’akari da raguwar farashin ɗanyen mai ta hanyar rage farashin fetur ga masu amfani.
Shugaban PETROAN na ƙasa, Mista Billy Gillis-Harry, ya ce raguwar farashin ɗanyen mai a duniya wata dama ce da ya kamata ta amfani wajen saukaka wa al’umma ta hanyar rage farashin fetur.
Sai dai Sakataren Yaɗa Labarai na ƙasa na ƙungiyar Masu Dillancin Man Fetur Masu Zaman Kansu ta Nijeriya (IPMAN), Chinedu Ukadike, ya ce akwai dalilai da dama da suka sa gidajen mai ba su yi gaggawar rage farashin su ba.
A cewarsa, matsalolin da suka shafi buƙata da samarwa, tare da haɗarin asarar kuɗaɗe, suna daga cikin manyan dalilan da ke hana masu kasuwancin sauke farashin fetur nan take.
Ya bayyana cewa dillalan da suka sayi fetur a tsohon farashi mai tsada ba za su iya rage farashin famfon su cikin gaggawa ba tare da fuskantar asara mai yawa ba.
Ukadike ya ƙara da cewa a ƙarƙashin tsarin kasuwar fetur mai ’yanci, babu wani tsari na gwamnati da ke diyya ga dillalai idan aka samu sauyin farashi kwatsam.
“Yawan kuɗin da ake buƙata domin sayen kayayyakin man fetur a yau ya fi yadda ake buƙata a baya sosai. Haka kuma kuɗin ruwa na rancen bankuna, kuɗin inshora da sauran kuɗaɗen gudanar da kasuwanci suna ƙara hauhawa,” inji shi.
Ya bayar da shawarar kafa Bankin Makamashi ko Bankin Man Fetur, wanda zai taimaka wajen samar da kuɗaɗen da ake buƙata wajen sayen kayayyakin man fetur tare da rage haɗarin da ke tattare da kasuwar.
Har ila yau, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta samar da ƙarin tallafi da tsare-tsare da za su taimaka wa dillalan mai masu zaman kansu domin tabbatar da cewa farashin fetur ya kasance mai saukin kai ga jama’a.
Ukadike ya jaddada cewa tashin farashin fetur na da tasiri kai tsaye ga dukkan ɓangarorin tattalin arziki, domin yana haifar da ƙarin kuɗin sufuri da hauhawar farashin kayayyaki.
Ya kuma yi kira da a farfaɗo tare da tabbatar da cikakken aiki na matatun mai na cikin gida, ciki har da Matatar Mai ta Fatakwal da Matatar Mai ta Kaduna, yana mai cewa hakan zai kara gasa a kasuwa, faɗaɗa hanyoyin samar da fetur da kuma taimakawa wajen daidaita farashi.
Masana tattalin arziki na ganin cewa duk da raguwar farashin ɗanyen mai a duniya, akwai buƙatar ƙarin matakai daga gwamnati da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa sauyin farashin ya kai ga masu amfani da fetur a Nijeriya.
