Masana sun bayyana dalilan asarar tiriliyoyin Naira a kasuwar hannayen jari

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Masana harkokin kasuwannin kuɗi sun bayyana cewa raguwar da ake gani a kasuwar hannayen jari ta Nijeriya a halin yanzu na da alaƙa da gyaran farashi bayan kamfanoni sun fitar da sakamakon kuɗaɗensu, hauhawar farashi da kuma taka-tsantsan da masu zuba jari ke yi yayin da ƙasar ke tunkarar babban zaɓen 2027.

Kasuwar hannayen jari ta ci gaba da fuskantar sauye-sauye a watan Yuni. Bayanai daga Kasuwar Hannayen Jari ta Nijeriya (NGɗ) sun nuna cewa NGɗ All-Share Indeɗ ya ragu da kashi 5.77 cikin ɗari daga farkon watan zuwa ranar 19 ga Yuni, 2026. Ma’aunin ya sauko daga maki 250,385.47 zuwa maki 234,941.27.

Haka kuma, jimillar darajar kasuwar ta yi asarar tiriliyan N9.182, inda ta sauko daga tiriliyan N160.509 zuwa tiriliyan N151.327 a daidai wannan lokaci.

Yayin da yake magana da manema labarai, Mataimakin Shugaban Kamfanin Highcap Securities Limited, David Adnori, ya ce akwai dalilai da dama da suka haddasa wannan koma baya, kuma babban abin da ake gani shi ne gyaran farashin hannayen jari da kasuwa ke yi bayan kamfanoni sun bayyana sakamakon ayyukansu na shekara.

A cewarsa, a irin wannan lokaci bayan an fitar da rahotannin kuɗi da sauran bayanan kamfanoni, kasuwa kan daidaita farashin hannayen jari da ainihin ƙimarsu da kuma yadda kamfanonin suka yi aiki.

Ya ce, kamfanonin da ba su cika tsammanin masu zuba jari ba kan fuskanci raguwar darajar hannayensu bayan wannan gyaran.

Adnori ya ƙara da cewa bayan kamfanoni sun raba ribarsu ga masu hannayen jari, rashin sabbin bayanan da za su iya motsa kasuwa kan janyo raguwar harkokin ciniki na ɗan lokaci, lamarin da ke haifar da saukar farashi.

Ya kuma nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki da aka samu a watannin baya-bayan nan, ko da yake ba ta da yawa, ta ƙara haifar da fargaba a tsakanin masu zuba jari.

A cewarsa, irin wannan yanayi na iya sa mutane su fara tunanin yiwuwar ƙarin tsauraran matakan kuɗi ko ƙarin kuɗin ruwa, wanda kan sa wasu su janye kuɗinsu daga kasuwar hannayen jari.

Masanin ya kuma ce wasu masu zuba jari na jiran fitowar hannayen jarin Kamfanin Matatar Dangote (IPO), abin da ya sa suka zaɓi ajiye kuɗinsu maimakon shiga kasuwa a halin yanzu.

Ya kuma bayyana cewa masu gudanar da harkokin kasuwa suna rage wasu jarin da suka mallaka domin kare kansu daga yiwuwar haɗarin siyasa yayin da Nijeriya ke ƙara kusantar babban zaɓe.

Duk da haka, Adnori ya bayyana cewa akwai kyakkyawan fata na farfaɗowar kasuwa nan gaba.

Ya ce, yayin da kamfanoni za su fara fitar da sakamakon rabin shekara a zangon uku na shekara, ana sa ran masu zuba jari za su sake nuna sha’awa ga hannayen jarin kamfanonin da suka yi kyakkyawan aiki.

A nasa ɓangaren, Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Kamfanin ECL Asset Management Limited, Charles Fakrogha, ya ce abin da ake gani yanzu wani ɓangare ne na tsarin ɗabi’ar kasuwa.

Ya ce, ba daidai ba ne a ce kasuwar na cikin mummunan yanayi, domin abin da ake gani gyaran kasuwa ne da ya zama dole.

Fakrogha ya bayyana cewa karɓar ribar da masu zuba jari suka samu na daga cikin manyan dalilan da suka haddasa raguwar farashin hannayen jari.

A cewarsa, mutane da dama sun samu ribar da ta kai matakin da suke so a bana, don haka suna sayar da wasu hannayen jarinsu domin cin gajiyar ribar da suka tara.

Ya kuma lura cewa fannin bankuna ya fi fuskantar matsin lamba, sakamakon sabbin manufofin da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ke shirin aiwatarwa domin kare masu ajiya da kuma ƙarfafa tsarin bankunan da ke ƙarƙashin tsarin Holdco.

A cewarsa, duk da cewa waɗannan sauye-sauyen na iya haifar da ɗan ruɗani a tsakanin masu zuba jari a yanzu, manufarsu ita ce ƙarfafa tsarin kuɗin ƙasar a nan gaba.

Fakrogha ya ce da zarar an fitar da sakamakon ayyukan kamfanoni na zangon biyu, masu zuba jari za su samu cikakkiyar fahimta game da tasirin waɗannan manufofi, wanda ka iya taimakawa wajen dawo da kwanciyar hankali da kuma ɗan bunƙasar kasuwa.

Ya jaddada cewa kasuwa tana tafiya ne cikin zagaye-zagaye, kuma wannan yanayin da ake ciki yanzu wani mataki ne kawai daga cikin tafiyar da kasuwa ke yi.

By ukarofi

Leave a Reply