“Kalaman jaruma Nafisa ba su da alaƙa da fim ɗin ƙaddara,” inji Abnur Entertainment
Daga AISHA ASAS
Yayin da ake ci gaba da samun ce-ce-ku-ce da martani daga ɓangarori daban-daban kan wasu kalamai da aka danganta da fitacciyar jarumar Kannywood Nafisa Abdullahi, kamfanin Abnur Entertainment, mai ɗaukar nauyin shirya fim din ‘ƙaddara’, ya fito karara ya fayyace matsayarsa kan lamarin.
A cikin wata sanarwa da kamfanin ya wallafa, ya bayyana cewa, kalaman da suka haddasa ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a ba su fito daga ɓangaren masu shirya fim ɗin ba, kuma ba su wakilci manufar fim ɗin ‘ƙaddara’ ko wani daga cikin masu ruwa da tsaki a aikin ba.
Kamfanin ya ce, abin da ta bayyana ra’ayi ne na mutum ɗaya, wanda aka furta bisa fahimta da aƙidar wanda ya yi maganar, don haka bai kamata a alaƙanta shi da fim ɗin ko kuma da waɗanda suka taka rawa wajen samar da shi ba.
Wannan bayani na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da tattaunawa a kafafen sada zumunta, inda wasu ke ƙoƙarin haɗa fim ɗin ‘ƙaddara’ da kalaman da aka da jarumar ta yi. Sai dai kamfanin ya wanke kansa daga wannan zargin, yana mai tabbatar da cewa, aikin da ya samar ba shi da wata manufa face nishaɗantarwa da faɗakar da al’umma ta hanyar fasaha.
Abnur Entertainment ya kuma jaddada matsayinsa na mutunta addinin Musulunci da sauran addinai, tare da girmama al’adu da kyawawan ɗabi’un al’umma. Kamfanin ya bayyana cewa, tun kafuwarsa yake ƙoƙarin samar da ayyukan da za su amfani jama’a tare da kiyaye abubuwan da al’umma ke kallon su a matsayin ginshikan tarbiyya da mutunci.
Sanarwar ta ƙara da cewa, duk wani aiki da kamfanin ke samarwa yana ƙarƙashin manufar ilmantarwa, faɗakarwa da nishaɗantarwa, ba tare da wata manufa ta tayar da husuma ko saɓani a tsakanin jama’a ba.
Daga ƙarshe, kamfanin ya yi kira ga mabiyansa da masu kallon fina-finansa da su yi hukunci bisa gaskiya da cikakken bayani, maimakon dogaro da raɗe-raɗi ko fassarar da ba ta samo asali daga tushen gaskiya ba. Har ila yau, ya buƙaci jama’a su ci gaba da nuna fahimta da haƙuri yayin da ake tattauna batutuwan da suka shafi harkokin nishaɗi da rayuwar fitattun mutane.
