
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Za a gudanar da taron tunawa a Abuja a ranar Litinin, 13 ga watan Yuli, 2026, domin karrama marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar 13 ga Yulin 2025.
Ana sa ran abokai, makusanta da masu fatan alheri su haɗu a babban birnin tarayyar domin yin addu’o’i da kuma tunawa da karamcinsa, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
An shirya wannan taro ne da nufin tunawa da hidimar da marigayin ya yi wa ƙasa, jagoranci da gudunmawarsa ga Nijeriya, bayan da aka yi masa jana’iza a mahaifarsa Daura ta Jihar Katsina a Yuli, 2025.
Tsohon shugaban ƙasar ya rasu ne bayan shafe shekaru 82 a duniya, a Landon yayin da yake karɓar magani a wani ƙaramin asibiti.
Daga bisani an dawo da gawarsa Nijeriya kuma aka mata jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
