
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Laraba ƙasar Ingila ta samu damar tsallakewa zuwa zagayen ‘yan 16 bayan doke Jamhuriyar Kongo da ci 2 da 1 a gasar Kofin Duniya da ke gudana a Nahiyar Amurka.
Da fari, Kongo ce ta samu damar jan ragamar wasan bayan zura ƙwallo guda ta hannun Brian Cipenga a minti na bakwai da fara wasan.
Daga bisani Harry Kane ya farke ana sauran minti 15 a kammala wasan, sannan ya kuma ƙara a minti na 86 duk ta hannun sabon ɗan wasan Barcelona Anthony Gordon, lamarin da ya ba Three Lions damar zuwa zagayen ‘yan 16.
A yanzu dai ƙasar za ta fafata da Mexico, wadda ta doke Ecuador a zagayen ‘yan 32.
