Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta amince da fitar da dala miliyan 27 a matsayin tallafin ƙarfafa aiki ga jihohin da suka cika ƙa’idojin shugabanci nagari da tsara kasafin kuɗi a ƙarƙashin Shirin Hope Governance, wanda Bankin Duniya ke tallafawa.
An sanar da hakan ne daga bakin Mai Kula da Shirin HOPE Governance na ƙasa, Assad Hassan, yayin wani taron bitar aiki da aka shirya wa Kwamishinoni, Manyan Sakatarori da Daraktocin Kasafi da Tsare-tsare daga jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja, wanda aka gudanar a Abuja ranar Talata.
Assad Hassan ya bayyana cewa an amince da sakin kuɗaɗen ne bayan Hukumar Tabbatar da Ayyuka Mai Cin Gashin Kanta ta Wucin Gadi (IVA) ta tantance yadda jihohin suka aiwatar da manufofin da aka shimfiɗa a matakin farko na shirin, wanda ake kira Year-Zero Disbursement-Linked Results (DLRs).
A cewarsa, jihohin Bayelsa, Borno, Kano, Kebbi da Yobe sun cancanci karɓar dala miliyan 1.5 kowacce bayan sun amince da cikakkun ƙa’idojin shirya da gabatar da haɗaɗɗun tsare-tsaren aiki na kasafin kuɗin ilimin bai ɗaya da kula da lafiya matakin farko.
Ya kuma bayyana cewa jihohin Adamawa, Bayelsa, Borno, Delta, Gombe, Kano, Filato, Taraba da Yobe sun samu cancantar karɓar dala dubu 500 kowacce saboda sun aiwatar da ƙa’idojin kasafi iri ɗaya tare da tsarin lissafin kuɗaɗen ƙananan hukumomi.
Haka kuma, Hassan ya ce jihohin Abia, Bayelsa, Borno, Edo, Ekiti, Enugu, Imo, Jigawa, Kano, Kebbi, Kogi, Nasarawa, Ondo, Filato da Yobe za su karɓi dala dubu 500 kowacce bayan sun wallafa kasafin kuɗin ‘yan ƙasa na shekarar 2025 da ya shafi ilimin bai ɗaya da kula da lafiya matakin farko.
Ya ƙara da cewa, jihohin da ba su samu wannan tallafi ba sun gaza ne saboda sun wallafa takardun da ake buƙata bayan wa’adin ranar 31 ga Maris, 2025, ko kuma ba su cika ƙa’idojin tantancewar ba, ko kuma sun kasa wallafa takardun a shafukansu na hukuma.
Har ila yau, Mai Kula da Shirin na ƙasa ya bayyana cewa ana sa ran Hukumar Tabbatar da Ayyuka Mai Cin Gashin Kanta ta Wucin Gadi za ta kammala mataki na biyu na tantancewar Year-Zero nan da watan Yulin 2026.
Shirin HOPE Governance wani shiri ne na dala miliyan 500 da Bankin Duniya ke tallafawa, wanda manufarsa ita ce inganta tsarin samar da kuɗaɗe, gaskiya da riƙon amana wajen gudanar da ayyukan ilimin bai ɗaya da kuma kula da lafiya matakin farko a faɗin Nijeriya.
