WhatsApp zai kawo tsarin amfani da suna da ɓoye lambar waya domin kare sirri

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kamfanin sadarwar zamani na WhatsApp, mallakin Meta, ya sanar da shirin ƙaddamar da sabon tsarin Suna, wato Username, wanda zai bai wa masu amfani damar yin hira da juna ba tare da bayyana lambobin wayarsu ba, a wani mataki da kamfanin ya ce zai ƙara ƙarfafa kariyar sirri a dandalinsa.

Sabon tsarin, wanda ake sa ran za a fara amfani da shi a duniya cikin watanni masu zuwa, zai bai wa sama da masu amfani biliyan uku damar haɗuwa da juna ta hanyar sunayen amfani na musamman maimakon musayar lambobin waya.

Kamfanin ya bayyana cewa daga ranar Litinin, masu amfani za su iya fara tanadin sunayen da suke so a manhajar, duk da cewa amfani da tsarin ba zai zama tilas ba.

A cewar WhatsApp, masu amfani za su iya sauyawa ko goge sunayen amfaninsu a duk lokacin da suka ga dama, yayin da kuma za a ci gaba da amfani da hanyoyin kariya da ake da su yanzu kamar toshe mutum ko kai rahoton waɗanda ke damun masu amfani.

An kuma bayyana cewa sunayen amfani ba za su wuce haruffa 35 ba, tare da sanya wasu ƙa’idoji domin hana kwaikwayon fitattun mutane da mashahuran jama’a.

Jami’ar da ke jagorantar bunƙasa kayayyakin WhatsApp, Alice Newton-Reɗ, ta ce an samar da wannan fasalin ne bayan karɓar ra’ayoyi daga masu amfani da manhajar da ke son samun wata hanya ta sadarwa ba tare da bayyana lambobin wayoyinsu ba, musamman a tattaunawar rukuni-rukuni.

Ta ce, “Mun ji daga bakin masu amfani cewa ba koyaushe suke son bayyana lambobin wayarsu ba domin ci gaba da hulɗa da wasu, musamman a rukunin tattaunawa.”

Newton-Reɗ ta ƙara da cewa kamfanin na fatan wannan sabon tsarin zai bai wa masu amfani cikakken iko kan yadda suke son bayyana kansu a WhatsApp.

Da zarar an kammala aiwatar da tsarin gaba ɗaya, lambobin wayar masu amfani ba za su kasance a bayyane ba yayin tattaunawar da aka kafa ta hanyar sunayen amfani. Sai dai kamfanin ya jaddada cewa har yanzu dole ne mutum ya mallaki lambar waya domin buɗe asusun WhatsApp.

Haka kuma, WhatsApp ya bayyana cewa ba za a samar da wani kundin sunayen amfani na jama’a ba da kowa zai iya bincikawa.

Wannan ci gaban na zuwa ne a daidai lokacin da ake sauyin shugabanci a WhatsApp, inda Kunal Shah zai karɓi ragamar jagorancin manhajar daga Will Cathcart, bayan ya shafe shekaru bakwai yana jagorantar kamfanin.

Masu lura da harkokin fasahar sadarwa na ganin cewa wannan sabon tsari zai taimaka wajen ƙara kare bayanan sirrin masu amfani, musamman waɗanda ke son tattaunawa da sababbin mutane ko shiga ƙungiyoyin tattaunawa ba tare da bayyana lambobin wayarsu ba.

By ukarofi

Leave a Reply