Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Majikiran Gona, Arc. Mohammed Abubakar Akko, ya yi kira ga gwamnatin jihar Gombe da ta inganta tsarin jin daɗin mambobin majalisar sarakuna da hakiman jihar, yana mai cewa ƙarfafa cibiyoyin gargajiya zai taimaka wajen bunƙasa zaman lafiya, tsaro da ci gaban al’umma.
Akko ya bayyana cewa sarakunan gargajiya na taka muhimmiyar rawa wajen sasanta rikice-rikice, tabbatar da zaman lafiya da kuma tallafa wa gwamnati a harkokin tsaro, don haka ya zama wajibi a samar musu da ingantaccen tallafi da kayan aiki domin sauƙaƙa musu gudanar da ayyukansu.
Ya yabawa gwamnatin jihar bisa gyaran da ake yi wa wasu fadodin sarakuna da hakimai ta hannun hukumar baɓaka ayyuka ta haɗin gwiwa (JDPA), yana mai cewa wannan mataki na taimakawa wajen kare al’adun gargajiya da kuma ɗaukaka martabar masarautu.
Sai dai ya jaddada buƙatar samar da ƙarin tallafi da ingantaccen tsarin walwala ga sarakuna da hakimai domin su ci gaba da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, musamman wajen sasanta rikice-rikice, tabbatar da zaman lafiya da kuma taimaka wa gwamnati wajen kula da tsaro.
Majikiran Gona ya kuma nuna damuwa kan matsalolin sufuri da wasu masarautu ke fuskanta, yana mai cewa hakan na nuna muhimmancin sake nazarin tsarin tallafin da ake bai wa sarakunan gargajiya.
Ya buƙaci masu kula da harkokin masarautu su gabatar wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya shawarar samar da cikakken tsarin jin daɗi ga sarakuna da hakimai, kwatankwacin abin da ake da shi a jihohin Bauchi da Taraba.
A cewarsa, zuba jari a cibiyoyin gargajiya wata muhimmiyar hanya ce ta ƙarfafa zaman lafiya, inganta tsaro da tabbatar da ci gaba mai ɗorewa a jihar Gombe.
