Kada ma’aikatan Katsina su damu bisa sabon tsarin fansho – Dakta Faruk

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban kwamitin gyaran tsarin fansho da gratuti na Jihar Katsina, Dr. Faruk Aminu, ya tabbatar wa ma’aikatan gwamnati cewa babu wani abin fargaba dangane da sabon tsarin fansho na gudunmawar ma’aikata (Contributory Pension Scheme).

Ya ce sabon tsarin zai tabbatar da tsaro ga kuɗaɗen fansho, tare da ƙara amincewa da yarda daga jama’a. Dr. Faruk Aminu ya bayyana haka ne a Katsina

A cewarsa, gwamnatin Dikko Umar Raɗɗa ce ya amince da sabon tsarin domin tabbatar da ɗorewar tsarin fansho ta hanyar rufe duk wata kafa ta almundahana da karkatar da kuɗaɗe.

Ya bayyana cewa sabon tsarin ya bambanta da tsohon tsarin da aka aro daga Jihar Jigawa, kuma an tsara shi ne domin amfanar ma’aikatan da suka yi shekaru biyar ko fiye da haka a aikin gwamnati.

Dr. Faruk Aminu ya ce domin tabbatar da cewa an kula da dukkan ma’aikata, gwamnati ta kafa hukumar kula da sauyin tsarin fansho ta Jiha da ƙananan hukumomi da kuma ofishin fansho na Jihar Katsina.

Ya ce hukumomin biyu suna aiki tare domin magance matsalolin bashin fansho da giratuti da aka daɗe ana fama da su.

A nasa ɓangaren, Darakta Janar na ofishin fansho na Jihar Katsina, Alhaji Nuraddeen Audi, ya yi cikakken bayani kan yadda sabon tsarin zai amfani ma’aikata yayin da suke aiki da kuma bayan sun yi ritaya.

Ya ce ma’aikatan da suka yi shekaru biyar ko fiye da haka a aiki za su riƙa bayar da wani kaso na albashinsu, yayin da gwamnati ma za ta bayar da nata gudunmawar, domin a tara kashi 20 cikin 100 na kuɗaɗen da za a biya su a matsayin gratuiti da fansho.

Haka kuma ya bayyana cewa a halin yanzu ofishin yana mayar wa wasu ma’aikata kuɗaɗen da aka cire musu a baya, bayan an tabbatar da cewa ba su cikin waɗanda sabon tsarin ya shafa.
Shi ma babban sakataren hukumar kula da sauyin tsarin fansho ta Jiha da ƙananan hukumomi, Alhaji Muntari Ammani, ya ce hukumar za ta ci gaba da kula da ma’aikatan da ba su shiga sabon tsarin fansho ba.

Ya kuma bayyana cewa kuɗaɗen da aka mayar wa wasu ma’aikata kwanan nan su ne kuɗaɗen da aka taba cire musu daga albashinsu tun farko.

Alhaji Muntari Ammani ya ce ɗaya daga cikin manyan nasarorin kwamitin gyaran tsarin fansho da giratuti ita ce samar da cikakken bayanan ma’aikatan gwamnati masu aiki da kuma waɗanda suka yi ritaya a faɗin jihar.

A nasa jawabin, shugaban majalisar gudanarwa ta hukumomin fansho guda biyu, Alhaji Ibrahim Boyi, ya jaddada cewa babu abin da ma’aikatan jihar za su ji tsoro a kansa dangane da sabon tsarin fansho.

Ya tabbatar da cewa gwamnatin Dikko Umar Raɗɗa za ta ci gaba da ɗaukar matakan inganta rayuwar ma’aikata tun suna aiki har zuwa bayan sun yi ritaya.

By ukarofi