Wanda ya yi silar ɗaukakar mu shine namu – Shugaban ƙungiyar ɗalibai

Spread the love

Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙaramar Hukumar Bichi ta gudanar da gagarumin taro a Sakatariyar ƙaramar hukumar domin jaddada aniyarta na cigaba da mara wa Ɗanmajalisar Tarayya mai Wakiltar Bichi, Alhaji Abubakar Kabir Abubakar baya, domin cigaba da inganta ilimin al’ummar yankin, musamman yara da matasa a ƙaramar hukumar.

A sanarwar da Jami’ar Yaɗa Labarai ta yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta raba wa manema labarai, Shugaban Ƙungiyar Ɗalibai na Bichi, Kwamared Mu’azzam Kabiru Adamu, ya bayyana gamsuwarsu ɗari bisa ɗari wajen mayar da alheri a gurbin alheri, dangane da irin yadda Ɗanmajalisar Tarayya na yankin ya jajirce na ganin kowane yaro ya rabauta da samun ingantaccen ilimi, ba tare da wariya ko bambanci ba.

Kwamared Mu’azzam, ya shaida duk wani ɗalibi ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Bichi da ya cancanta, tsawon shekaru (6) tun da Ɗanmajalisar ya fara jagoranci zuwa yanzu yake biya wa ɗalibai kusan mutum dubu hamsin 50,000 kuɗin makaranta a ciki da wajen kasar nan.

A bisa haka Kwamared, ya ayyana matuƙar jin daɗinsu tare da ɗimbun godiya ga Alhaji Abubakar Kabir Abubakar Bichi, bisa wannan babbar kadara ta samar da ilimi da yake tallafa musu, domin haskaka rayuwarsu ta hanyar gina rayuwar tasu da za su iya gogayya da kowa a faɗin duniya.

“Wanda yake yi mana shi ne namu, in Allah ya yarda ɗaliban Ƙaramar Hukumar Bichi za mu ba da cikakken goyon baya ga mai girma Ɗanmajalisar Tarayya a zaɓe mai zuwa; ba ma shi kaɗai ba, duk wanda ya ce mu zaɓa daga kan Shugaban ƙasa, Gwamna, Sanata, Ɗanmajalisar Tarayya da na jiha, mu a matsayinmu na ɗaliban ƙaramar hukumar Bichi sama da dubu hamsin, wanda ni a matsayina na Shugaban ɗalibai da nake jagoranta, su za mu zaɓa.” Kwamared Mu’azzam Kabiru Adamu.

Kazalika, Shugaban Ɗaliban da Ɗanmajalisar Tarayya Alhaji Abubakar Kabir Abubakar yake Ɗaukar Nauyin Karatunsu a faɗin Nijeriya, Kwamared Abdul-Aziz Umar Lawan, ya ce, Ɗanmajalisar a tun farko burinsa shi ne jaddada ilimin al’umma da kuma ƙarfafa shi a tsakanin al’ummarsa, duba da ilimi ne matakin farko dake wanzar da al’umma ta gari, sakamakon haka ya mayar da ilimi kyauta gami da tsayawa kai da fata wajen assasa harkokin ilimi a ɗaukacin ƙaramar hukumar.

” Ilimi da ya samar a ko’ina, Alhamdu lillahi ɓangaren tarbiyya kin ga ɗalibi shi ne mutum na farko mai tarbiyya; a makaranta ba ilimi kaɗai ake koyarwa ba, ana koyar da abin da bature yake cewa ( character and learning ) za ka koyi tarbiyya ne da ilimi a tare.” Kwamared Abdul-Aziz Umar Lawan.

A ɓangaren matan yankin, Ɗaliba Bikisu Yusuf, ta bayyana haƙiƙa kamar yadda maza suke samun tagomashin ilimi kyauta a yankin, haka dukkan mata suke rabauta da wannan tallafi na Ɗanmajalisar, kuma sun yi alƙawarin a shirye suke wajen amfanar da ilimin da suka samu a cikin al’umma.

“Dukkan ‘ya macen da ta samu ilimi, za ta jajirce wajen ganin “ya’yanta su ma sun samu, kuma za ta tarbiyantar da su, mahaifinsu ba zai shiga cikin wata damuwa ba idan ba ya nan, saboda ya san mahaifiyarsu tana da iilimi.” Bilkisu Yusuf.

By Babaji