
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar yaƙin naman zaɓe ta Mohammed Nakudu da Mallam Ibrahim Ringim ta jam’iyyar ADC ta yi watsi da ƙorafin da aka yi wa ɗan takarar gwamnanta na Jihar Jigawa, Sanata Sabo Nakudu, tana mai bayyana hakan a matsayin “cin fuska, ɓatanci da kuma makircin siyasa”.
Rahotanni sun bayyana cewa, ƙungiyar ta ce wasu mutum biyu, wato Abubakar Sani da Ibrahim Mai Jama’a ne suka sanya wa ƙorafin hannu wadda aka fitar a ranar 7 ga Yuli, 2026, inda suka yi iƙirarin cewa su ‘yan ADC ne daga Ƙaramar Hukumar Gwaram da ke Jihar.
A sanarwar da ke ɗauke da sanya hannu Sakataren yaɗa labaranta, Mati Ali, ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Sabo Mohammed Nakudu da Mallam Aminu Ibrahim Ringim, ta zargi waɗanda suka shirya ƙorafin da haifar da saɓani da ruɗar da jama’a yayin tunkarar babban zaɓen 2027.
A cewarta, ƙorafin, wanda aka yi wa take da “Ƙorafi Akan Sanata Sabo Nakudu, ɗan Takarar Gwamna a Jihar Jigawa..”, wani Mallam Bello Zaki daga Ƙaramar Hukumar Kazaure ne ya yaɗa shi, wanda kuma na hannun dama ne ga ɗaya daga cikin jiga-jigan da suka kafa jam’iyyar ADC a jihar.
Ƙungiyar ta ce, ababen da takardar ƙorafin ta ƙunsa ba gaskiya ba ne, ƙarya ce da ɓatanci da ke ƙoƙarin zubar da mutunci da darajar Sanata Nakudu a matsayinsa na mai kima a idon al’ummar yankinsa da ma jihar baki ɗaya.
Haka kuma, ƙungiyar yaƙin neman zaɓen ta yi zargin cewa wasu mutane ne suka kitsa makirci ga ɗan takarar gwamnan ganin yadda ya samu karɓuwa acikin jama’a.
Kazalika, ta yi zargin cewa karɓuwar da ADC ta samu yayin tunkarar zaɓen 2027 ya sa ana kai wa ɗan takarar nata hare-hare don ganin an haddasa wa harkokin siyasar tsaiko.
Har ila yau, ta ce ba a taɓa samun Sanata Nakudu da hannu a aikata laifukan da suka shafi rashawa ko wasu manyan laifuka ba, kuma a duba tarihin jagorancinsa na siyasa da kasuwanci, waɗanda acewarta sun taimaka wa samar da ayyukan ci-gaban jihar.
A ƙarshe, ta yi gargaɗi ga mutane ko ƙungiyoyin da suke da hannu a ƙorafin da cewa za su shigar da ƙara domin bayar da kariya ga mutuncin ɗan takarar nata.
