
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ministan Abuja Nyesom Wike, ya bayyana zarge-zargen da ake danganta wa Shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban, Femi Gbajabiamila akan batun hukumar bogi ta PFIPC a matsayin siyasa.
Wike ya bayyana haka ne a wata hira da ‘yan jarida ta wata-wata a ranar Alhamis, inda ya yi watsi da dukkan wani yunƙuri na ɓata manyan masu taimaka wa Shugaba Bola Tinubu.
Ministan ya kuma bayyana zargin Frins Adeniyi Adeyemi Matthew, wanda ya yi iƙirarin gudanar da PFIPC, akan Gbajabiamila a matsayin ƙarya da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da jama’a.
A ɗaya gefen, Gbajabiamila ya fitar da sanarwar barrantarwa inda ya ce babu wata hukumar Gwamnatin Tarayya mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC), lamarin da ya sa Adeyemi ya mayar da martani da cewa ai an sanya ta cikin kasafin ƙasa.
Akan haka ne Tinubu ya umarci Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) da ta gudanar da bincike mai zurfi acikin kwana 30 akan al’amarin.
A cewar Wike, an jingina maganar da Gbajabiamila ne saboda an san cewa matuƙar aka ɓata sunan Shugaban ma’aikatan Fadar, to hakan zai iya zame wa gwamnatin cin fuska.
Kazalika, ministan Abujan ya yi wa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar da wasu martani akan kira a tsige Gbajabiamila, yana mai jaddada goyon bayansa akan binciken ICPC da Shugaba Tinubu ya umarci a yi akan lamarin.
