Dangote zai gina babbar matatar mai a Kenya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Rukunin Kamfanonin Dangote ya bayyana shirinsa na samar da kuɗaɗen gina sabuwar matatar mai mai ƙarfin tace ganga 700,000 a kowace rana a ƙasar Kenya, ta hanyar haɗa kuɗaɗen shiga na cikin gida, fitar da takardun bashin gwamnati da kuma kuɗaɗen da ake sa ran samu daga sayar da hannayen jari ga jama’a (IPO).

Sabuwar matatar, wadda za a gina a Tsibirin Lamu da ke gabar tekun Kenya, ana sa ran za ta kasance mafi girma a Gabashin Afirka, tare da taimakawa wajen ƙarfafa tsaron makamashi a yankin ta hanyar rage dogaro da shigo da tataccen man fetur daga ƙasashen waje.

Rahoton kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce ana sa ran aikin zai ɗauki kusan shekara uku kafin a kammala shi, kuma zai riƙa samar da tatattun kayayyakin man fetur ga Kenya da sauran ƙasashen maƙwabta.

Wannan mataki na daga cikin dabarun Rukunin Kamfanonin Dangote na faɗaɗa harkokin tace mai a faɗin Afirka, bayan fara aikin matatar mai ta Legas mai ƙarfin tace ganga 650,000 a kowace rana.

Mataimakin Shugaban Sashen Mai da Iskar Gas na Dangote Industries, Edwin Deɓakumar, ya bayyana cewa an riga an fara wasu ayyukan farko na shirin. Ya ce, an zaɓi wurin da za a gina matatar, ana gudanar da gwajin aasa, yayin da aikin zane da ƙirar fasahar ginin ya fara. “A tun farko Kenya ce muka zaɓa domin wannan aiki,” inji Deɓakumar.

Ya ƙara da cewa, za a samu kuɗaɗen aikin ne daga kuɗaɗen shiga na kamfanin, takardun bashi (bonds) da kuma kuɗaɗen da za a samu daga shirin fitar da hannayen jarin kamfanin kasuwa. Sai dai bai bayyana takamaiman kuɗin da aikin zai lashe ba, amma ya ce zai yi daidai da kuɗin da aka kashe wajen gina Matatar Dangote da ke Legas.

Matatar Dangote, wadda hamshaƙin attajirin Afirka Aliko Dangote ya gina, ta lakume sama da dala biliyan 20 kafin ta fara aiki a hukumance a shekarar 2024, duk da cewa a shekarar 2013 an kiyasta za ta ci kusan dala biliyan tara kacal.

An ce, ƙarin kuɗin ya samo asali ne sakamakon sauya wurin aikin, ƙalubalen fasaha, faɗuwar darajar Naira, matsalolin da annobar COVID-19 ta haifar da kuma hauhawar farashi a duniya. Sabuwar matatar da za a gina a Kenya za ta kasance babbar jarin tace mai da Dangote ya taɓa yi a wajen Nijeriya, lamarin da ke nuna burinsa na zama babban mai samar da tatattun kayayyakin man fetur a nahiyar Afirka. Rahoton ya kuma nuna cewa a baya Dangote ya taɓa duba yiwuwar gina matatar mai a tashar jiragen ruwa ta Tanga da ke Tanzania, amma daga bisani ya karkata hankalinsa zuwa Kenya bayan nazarin abubuwan more rayuwa, hanyoyin sufuri da kuma damar kasuwanci.

By ukarofi

Leave a Reply