Samun nasarar hukunta mutum 150 da aka samu da laifukan ta’addanci cikin kwanaki biyu kacal ya zama wani babban ci gaba a tsarin shari’ar Nijeriya. Wannan mataki ya nuna cewa Gwamnatin Tarayya ta fara ɗaukar yaƙi da ta’addanci da muhimmanci, tare da ƙoƙarin tabbatar da cewa masu aikata irin waɗannan manyan laifuka sun fuskanci hukunci cikin gaggawa.
Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ya bayyana cewa a sabon zagayen shari’ar da aka gudanar a Abuja, an saurari shari’o’i kusan 160, inda aka samu hukuncin ɗaurin laifi ga kusan mutum 150.
Ya kuma buƙaci al’umma su ci gaba da nuna haƙuri yayin da gwamnati ke ci gaba da gudanar da wannan shiri domin tabbatar da adalci, ɗaukar alhaki da bin doka.
Wannan ya biyo bayan wani zagaye na baya da aka yi tsakanin 7 zuwa 10 ga Afrilu, inda aka gurfanar da sama da mutum 500 da ake zargi da ta’addanci. Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da wannan tsarin ne domin rage tarin shari’o’in ta’addanci da suka daɗe ba a yanke musu hukunci ba.
A baya-bayan nan kuma, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi gargaɗi mai ƙarfi ga ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da masu ɗaukar nauyinsu da su miƙa wuya ko kuma su fuskanci ƙarfin doka. Haka kuma ya sanar da ɗaukar sabbin ‘yan sanda sama da 50,000 da dubban sojoji domin ƙarfafa yaƙi da rashin tsaro.
Sai dai wannan yunƙuri ba na gwamnatin tarayya kaɗai ba ne. Wasu gwamnonin jihohi ma sun fara ɗaukar matakai masu tsauri wajen yaƙar ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga.
ɗaya daga cikin misalan da suka fi ɗaukar hankali shi ne yadda gwamnatin Jihar Kogi ta sanar da kashe fitaccen shugaban ‘yan bindiga, Kachala Ibrahim Batijo, wanda ake zargi da jagorantar hare-hare da dama, ciki har da yunƙurin kai hari wata makaranta a Iluke Bunu da ya yi sanadin mutuwar mutane uku.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Sadarwa na Jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ya ce an samu wannan nasara ne sakamakon haɗin gwiwar jami’an tsaro daban-daban da kuma amfani da na’urorin tattara bayanan sirri na zamani. A cewarsa, jami’an tsaro sun daƙile yunƙurin sace ɗalibai, sannan suka kashe Batijo da wasu daga cikin mayaƙansa.
Jaridar Blueprint Manhaja ta yaba da matakan da Gwamnatin Tarayya da gwamnatin Jihar Kogi ke ɗauka wajen yaƙi da ta’addanci da sauran matsalolin tsaro da suka jawo asarar rayuka da dukiyoyi masu tarin yawa a ƙasar nan.
Sai dai muna kira ga sauran gwamnonin jihohi da su ɗauki irin wannan matakin na nuna ƙwazo wajen tinkarar matsalar tsaro, nuna sassauci ko sulhu da ƙungiyoyin ta’addanci bai taɓa samar da sakamakon da ake buƙata ba. A ra’ayin wannan jarida, wajibi ne gwamnati ta ci gaba da ɗaukar tsauraran matakan doka domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
