Kiran kanku lauyoyi zai janyo muku kora – Makarantar lauyoyi ga ɗalibanta

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Majalisar Ilimin Shari’a ta Makarantar Lauyoyi ta Nijeriya ta gargaɗi ɗaliban da ke jiran bikin rantsuwar kama aikin lauya, wato bar, da su guji sanya kayan aikin lauya tare da bayyana kansu a matsayin cikakkun lauyoyi kafin a hukumance a karɓe su cikin ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya.

Rahoton ya nuna cewa wannan gargaɗi na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakatariyar Majalisar Ilimin Shari’a kuma Daraktar Gudanarwa, Aderonke Osho, ta sanya wa hannu, wadda Makarantar Horar Da Lauyoyi Ta Nijeriya ta fitar a ranar Talata.

Majalisar ta bayyana cewa ta lura da yadda wasu masu jiran shiga aikin ke ƙara yaɗa katunan gayyata, hotuna da bidiyoyinsu sanye da cikakkun kayan aikin lauya, wato hular lauya da rigar lauya, tare da bayyana kansu a matsayin ƙwararrun lauyoyi a shafukan sada zumunta.

Haka kuma, Majalisar ta nuna damuwa kan yadda wasu daga cikin waɗannan ɗalibai ke kiran kansu da “Barristers and Solicitors of the Supreme Court”, tare da liƙa wa sunayensu laƙabin “Esquire (Esq.)” tun kafin a kammala shigar da su cikin ƙungiyar lauyoyi.

Majalisar ta jaddada cewa irin wannan ɗabi’a ta saɓa da tanade-tanaden Sashe na 22 na Dokar Masu Aikin Lauya (Legal Practitioners Act), wadda ta fayyace waɗanda doka ta amince su gudanar da aikin lauya a Nijeriya.

Har ila yau, Majalisar ta yi Allah-wadai da yadda wasu ke sanya hular lauya da rigar lauya tare da tufafin da ba su dace ba ko kuma waɗanda ba tsarin sana’ar ya tanada ba, tana mai cewa hakan ya saɓa wa mutunci, ladabi da al’adun sana’ar lauya.

A cewar sanarwar, wannan hali ya kuma karya Dokar 45 ta ƙa’idojin Da’a Ga Masu Aikin Lauya a Nijeriya (Rules of Professional Conduct). Sanarwar ta ce, “Majalisar Ilimin Shari’a da Makarantar Horar Da Lauyoyi Ta Nijeriya sun lura da wani mummunan yanayi da ke ƙaruwa, inda masu jiran shiga Bar ke yaɗa hotuna, bidiyo da katunan gayyata suna sanye da cikakkun kayan aikin lauya, tare da bayyana kansu a matsayin ƙwararrun lauyoyi a kafafen sada zumunta.”

Saboda haka, Majalisar ta umarci duk wanda abin ya shafa da ya gaggauta goge duk wani rubutu, hoto, bidiyo ko wani abu makamancin haka da ya wallafa a kafafen sada zumunta ko wasu dandalan intanet da ya saɓa wa waɗannan ƙa’idoji.

Ta kuma yi gargaɗin cewa duk wanda ya ƙi bin wannan umarni na iya fuskantar hukuncin ladabtarwa, wanda zai iya shafar cancantarsa da dacewarsa wajen shiga ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya.

Majalisar ta ƙara da cewa, “Ana umartar duk masu neman shiga Bar da suka karya waɗannan ƙa’idoji da su cire nan take duk wani rubutu, hoto, bidiyo ko wani abu da ya saɓa wa dokoki daga kafafen sada zumunta da sauran dandalan intanet.”

Ta yi gargaɗin cewa rashin bin wannan umarni na iya haifar da hukuncin ladabtarwa, tare da jefa cancantar ɗan takara na shiga aikin lauya cikin haɗari.

By ukarofi