
Daga BELLO A. BABAJI
Jagoran Addinin Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei ya ci alwashin ramuwar halaka mahaifiyinsa kuma magabacinsa a shugabancin ƙasar, marigayi Ayatollah Ali Khamenei da aka yi a watannin baya, yana mai cewa waɗanda ke da hannu a kisan za su girbi abin da suka shuka.
An bayyana haka ne a babban gidan talabijin na Iran a ranar Asabar tun bayan fara jana’izar mahaifin nasa mako guda da ya gabata.
A wata sanarwa da aka fitar, jagoran ya ce lallai ba iya Iran kaɗai za ta nemi a adalci akan al’amarin ba, har ma da sauran mutanen duniya, lamarin da ya ƙarfafa fargaba a yankin Gabas ta Tsakiya da ke fama da matsalolin rikici.
“Mun ƙudirci ramuwa akan jinin shahidin jagoran da dukkan waɗanda suka yi shahada a yaƙe-yaƙe biyun nan daga azzalumai da muggan makasa”, inji sanarwar.
Waɗannan kalamai na zuwa ne a daidai lokacin da Iran ke fuskantar tasirin ƙalubalen siyasa da shugabanci na rashin Ayatollah Ali Khamenei da kuma rikicin da ke tsakaninta da Amurka da Isra’ila.
Kisan, a yayin musayar wuta, ya sauya Ali Khamenei a matsayin shugaban ƙasar bayan shafe tsawon shekaru 37 akan karagar mulki, wanda ya kasance ɗaya daga cikin masu faɗa-a-ji a shiyyar Gabas ta Tsakiya.
