Wata mata ta ɓoye kwarto cikin jakar Ghana-must-go a Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Jami’an hukumar Hisbah ta jihar Kebbi sun kama wani mutum da aka gano yana ɓoye a cikin ƙaton buhun nan na “Ghana-Must-Go” a gidan wata matar aure da ke unguwar Badariya a birnin Kebbi.

Daraktan Shari’a na hukumar Malam Sirajo Kamba, ya bayyana cewa hukumar ta kai samame ne a gidan bayan samun bayani ne daga mazauna unguwar ne inda suka sandar da hukumar cewa sun ga wani mutum ba su yarda da salon da ya ɗauka na shiga gidan ba da misalin ƙarfe 12:15 na daren ranar Litinin ɗin da ta gabata sai suka yanke shawarar sanarda hukumar.

Saboda yanayin da a ke ciki ya sa hukumar ba ta yi ƙasa a gwiwa ba ta isa gidan, daga farko matar ta ƙaryata zargin sai dai bayan mahawara mai ƙarfi daga baya ta amince da su shiga su bincika.
A cikin binciken ne suka ga wani ƙaton jakar Ghana must go suna duba ta sai ga mutum a ciki.

Binciken da hukumar ta gudanar ya nuna cewa akwai alaƙar soyayya ta haram tsakanin mutumin da matar auren.
Kamba ya ce duka mutanen biyu sun amsa laifinsu yayin tambayoyi, kuma za a miƙa su zuwa kotu domin fuskantar shari’ar Musulunci.

By ukarofi