Sojoji sun miƙa ɗalibai da malaman Oriire da aka ceto ga gwamnatin Oyo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar Sojin Nijeriya ta miƙa ɗalibai da malaman nan da aka sace na makarantu a yankin Oriire da ke Jihar Oyo ga gwamnatin jihar a hukumance bayan kammala aikin duba lafiyarsu da nazari a kai a sa’ilin da aka ceto su.

A ranar, Juma’a, 10 ga Yuli, 2026 ne suka shaƙi iskar ‘yanci bayan shafe kwanaki 56 a hannun ‘yan bindiga. An damƙa su ne bayan sama da kwanaki biyu ana musu magani a Asibitin Shiyya ta 2 ta hedikwatar Rundunar Sojin da ke Barikin Odogbo a Ibadan.

Wannan na nufin kawo ƙarshen aikin sojoji na ba su kulawar da ta dace bayan ceto su daga hannun ‘yan garkuwar da kuma alamta mafarin koma wa iyalansu da yankunansu a ƙarƙashin sanya idon gwamnatin Oyo.

Da take jawabin bayan ceto su, ɗaya daga cikin waɗanda iftila’in ya afka wa, Misis Alamu, ta bayyana godiyarta ga gwamnati, hukumomin tsaro da al’ummar Nijeriya bisa ƙoƙarinsu wajen samun ceto su daga halin.

Ta bayyana irin ƙalubalen da suka fuskanta a lokacin da suke hannun ‘yan bindigar waɗanda daga ciki akwai faɗa musu da ‘yan bindigar ke yi cewa gwamnati da al’umma sun kawar da kai daga halin nasu.

Ta ƙara da cewa, an taɓa samun lokacin da suka shiga fargabar akwai yiwuwar a rasa su bayan rasa wasu daga cikinsu a yayin da suke komar masu garkuwar.

Kazalika, ta yi zargin ‘yan bindigar sun halaka wasu daga cikinsu da nufin tilasta wa gwamnati yin hoɓɓasa a ƙoƙarinta na ganin an ceto su.

Har ila yau, ta yi wa Shugaba Bola Tinubu godiya, Gwamna Seyi Makinde, jami’an soji, jami’an tsaro da kuma ‘yan Nijeriya bisa ƙoƙarinsu na tabbatar da cewa an ceto su cikin ƙoshin lafiya.

By Babaji

Leave a Reply