
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya shigar da ƙara a kotu akan Frins Adeniyi Adeyemi Matthew da ake zargi da bayyana kansa a matsayin Darakta Janar na hukumar bogi ta PFIPC akan zargin sa da yaɗa kalaman ɓata suna.
A cikin ƙarar, wadda Gbajabiamila ya shigar a Babbar Kotun Tarayya, ya buƙaci a tilasta wa wanda ake ƙara ya biya shi diyyar Naira biliyan 15.2 na dameji, yana mai cewa zarge-zargen da aka yi masa na neman cin hanci ƙarya ne da ta janyo masa zubewar mutunci da martabarsa a idon al’umma.
Akan haka ne ya nemi kotun da ta umarci Adeyemi da ya janye kalaman tare da neman afuwa a fili, yana mai jaddada cewa zarge-zargen da ya ɗora masa ba su da asali.
Rahotanni sun bayyana cewa, Adeyemi ya alaƙanta Gbajabiamila da zargin yunƙurin amfani da hukumomin tsaro akansa da kuma yin iƙirarin marigayi Babatunde Tanimola a matsayin wanda ya shiga tsakaninsa da shugaban ma’aikatan.
Saidai, a jawabin da ya gabatar a ƙarar Gbajabiamila ya musanta dukkan zarge-zargen a matsayin ƙarya da aka ƙirƙira da ba su da tushe ko makama.
