Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Hana Sha da Safarar Muggan ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta kama wasu muggan kwayoyi da ake zargin nau’in Canadian Loud ne, masu nauyin kilo 4,143.5, waɗanda aka ɓoye cikin buhuna 8,287 a tashar jiragen ruwa ta Apapa da ke Jihar Legas.
Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
A cewarsa, an kama muggan kwayoyin ne a cikin wani kwantena da aka shigo da shi daga ƙasar Kanada zuwa Nijeriya, inda jami’an NDLEA suka gudanar da aikin tare da haɗin gwiwar Hukumar Kwastam da sauran jami’an tsaro a ranar 10 ga watan Yuli.
Babafemi ya ce kimar muggan kwayoyin da aka kama ta kai Naira biliyan 10.3, yayin da nasarar ta samu ne sakamakon tsauraran matakan sa ido da bibiyar kayan tun daga lokacin da suka tashi daga birnin Montreal na ƙasar Kanada.
Ya ƙara da cewa jami’an NDLEA da ke aiki ƙarƙashin rundunar ta musamman ta DOGI sun kuma kama wani fitaccen mai safarar miyagun ƙwayoyi, lamarin da ya taimaka wajen dakile yunƙurin fitar da wasu muggan kwayoyi masu nauyin kilo 2.5, ciki har da nau’in Skunk, wanda ke cikin rukunin tabar wiwi (Cannabis).
A cewarsa, an ɓoye waɗannan kwayoyin ne a cikin tukunyar iskar gas da aka shirya fitarwa daga Nijeriya zuwa ƙasar Cyprus.
Babafemi ya bayyana cewa jami’an NDLEA a faɗin ƙasar nan na ci gaba da gudanar da shirye-shiryen wayar da kan jama’a kan illolin da ke tattare da safara da kuma amfani da miyagun ƙwayoyi a makarantu, coci-coci, masallatai, wuraren aiki da kuma al’ummomi daban-daban.
Ya kuma ce shugaban hukumar, Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa (mai ritaya), ya yaba da ƙoƙarin jami’an NDLEA, musamman waɗanda ke aiki a ƙarƙashin rundunar DOGI da kuma jami’an da ke tashar jiragen ruwa ta Apapa.
Marwa ya buƙaci jami’an hukumar da su ƙara zage damtse wajen hana shigowa da kuma yaɗuwar miyagun ƙwayoyi a duk faɗin Nijeriya.
