
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dakarun sashe na 6 da ke aiki a ƙarƙashin Atisayen Enduring Peace, sun yi nasarar kama wani da ake zargin ƙasurgumin ɗan dabar masu garkuwa da mutane ne da aka alaƙanta da wasu hare-hare da garkuwa akan babban titin Jos zuwa Makurɗi a Jihar Filato.
Masanin harkar tsaro, Zagazola Makama ne ya sanar da haka a wani saƙo da ya wallafa a shafin X a ranar Juma’a.
A cewar rubutun, an kama wanda ake zargin ne da misalin ƙarfe 5 na yammacin ranar 16 ga watan Yuli yayin wani atisaye da dakarun suka ƙaddamar a yankin sansaninsu na ƙauyen Bangai da ke Ƙaramar Hukumar Riyom.
An ruwaito cewa, atisayen wani ɓangare ne na ƙoƙarin sojoji na daƙile ayyukan ‘yan ta’adda da ƙarfafa tsaro a babbar hanyar.
Bincike ya nuna cewa, wanda ake zargin mamba ne daga cikin wata babbar dabar ‘yan ta’adda da ake zargi da matsa lamba ga masu zirga-zirga a ababen hawa da mazauna ta hanyar garkuwa da wasu munanan hare-hare.
A halin yanzu ɗan bindigar na hannun sojoji, inda ake kan gudanar da bincike akansa.
A cewar majiyoyi, ɗan ta’addar yana bai wa masu bincike muhimman bayanai da za su taimaka wa ƙoƙarinsu wajen daƙile ayyukan ta’addanci da kuma kamo sauran ‘yan dabarsu da ake nema ruwa a jallo.
