
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, ya kirayi mambobin jam’iyyar APC a Jihar Neja da su sulhunta rikice-rikicen da ke tsakanin wasu daga cikinsu tare da haɗa kansu da girmama juna domin ƙarfafa lamuran jam’iyyar da harkokin dimukraɗiyya a Nijeriya.
A wata sanarwa da Mai taimaka wa ministan akan lamuran Bincike da Dabaru, Saidu Ahmed ya fitar, ministan ya yi wannan kira ne a ranar Asabar, yayin ganawa da masu ruwa da tsaki na jihar a wani zama da Gwamna Umaru Bago ya jagoranta a Gidan Gwamnatin Neja.
Da yake jawabi ga mambobin, Minista Idris ya buƙaci masu ruwa da tsakin da su jingine dukkan wani bambance-bambance da ke tsakaninsu tare da yin aiki tare don maslahar jam’iyyar, jihar da ma ƙasa baki ɗaya.
A cewarsa, dimukraɗiyya na yin nasara ne yayin da jagorori suka fifita amfaninta sama da buƙatun ƙashin kansu, yana mai cewa nasarar da APC ke samu a matakin ƙasa da jiha sun dogara ne da tattaunawa, damawa da kowane ɓangare da kuma fahimtar juna a matakin cikin gida.
Ya kuma yaba wa Gwamna Bago bisa kiran zaman, yana mai bayyana hakan a matsayin abin da aka yi a lokacin da ya dace da kuma bayar da damar sulhu da sabunta muhimman salon gudanar da ayyukan da APC ta sanya a gaba.
Wannan kira na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun siyasa ke cigaba da shirya wa tunkarar babban zaɓen 2027 da ke tafe a Nijeriya.
