Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Hukumar hisba ta jihar Kebbi ta sanar da tsintuwar wani jinjiri bayan wani otel a cikin garin Birnin Kebbi. Daraktann shari’a Malam Surajo Usman Kamba ya bayyana cewa bayan da hukumar hisbah ta sami rahoton wani jinjiri da a ke sa ran an jefar da shi ne a bayan Zinari Hotel da ke cikin garin Birnin Kebbi, ba ta yi ƙasa a gwiwa ta tura jami’an ta zuwa wajen. Bayan da suka isa wajen sun tarar da jinjirin cikin yanayi mai buƙatar kulawa, inda aka ceto shi tare da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da lafiyar sa da kuma kare haƙƙin sa.
Ya ce tuni an miƙa jinjirin ga hukumar da ta dace domin cigaba fa kulawa da shi. Yayin da kuma a ɗaya ɓangaren, hukumomin tsaro suka fara bincike domin gano waɗanda ke da hannu a wannan lamari.
Ya ƙara da cewa hukumar hisbah tana kira ga al’umma da su cigaba da bayar da haɗin kai ta hanyar kai rahoton duk wani abu da zai taimaka wajen kare rayuka da mutuncin al’umma. Haka kuma, hukumar tana jan hankalin iyaye da masu kula da yara da su kasance masu kula da tarbiyya da kuma neman mafita ta halal ga duk wata matsala, maimakon aikata irin wannan mummunan aiki da ya saɓawa koyarwar addinin musulunci da dokar ƙasa.
