Me yake kawo rashin zuwan yara makaranta a Arewa?

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A cikin wannan mako mai ƙarewa na samu damar halartar wani taron masu ruwa da tsaki kan harkokin ilimi, domin tattauna yadda za a ƙarfafa gwiwar iyayen yara, da samar da sabbin dabaru kan yadda za a daina cire yara daga makaranta zuwa aikin gona, ko aikin haƙar ma’adinai da neman kuɗi.

Hukumar Kula da Ilimin ƙananan Makarantu ta SUBEB a Jihar Filato tare da haɗin gwiwar UBEC da ke ƙarƙashin gwamnatin tarayya, da Kwamitin Kula da Harkokin Makarantu na SBMC ne suka gudanar da wannan taro, wanda ya tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi cigaban harkokin ilimi a makarantun gwamnati. 

Shugaban Hukumar SUBEB a Jihar Filato, Sunday Amuna ya nuna takaicinsa game da yadda makarantun firamare da ƙananan makarantun sakandire ke cigaba da zaizayewa babu ɗalibai, saboda bayyanar aikin ma’adinai a ƙauyuka da birane, da kuma saukar damina, inda wasu iyayen ke fifita aikin gona a maimakon zuwa makaranta.

Wani rahoto da Hukumar Majalisar ɗinkin Duniya ta UNESCO ta fitar a shekarar 2024 ya bayyana tasirin lalacewar wannan matsala sosai, inda aka nuna Nijeriya ce ke kan gaba a duniya kan matsalar yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta, suna gararamba a titi ko suna zuwa aikin ƙwadago da sunan neman kuɗi. An ƙiyasta akwai kimanin yara miliyan 18 da dubu 300 da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya, adadin da ya zarta na kowacce ƙasa a duniya. A cikin waɗannan yara dake tsakanin shekarun zuwa makaranta, miliyan 10 da dubu 200 ya kamata suna makarantun firamare ne, yayin da miliyan 8 da dubu 100 ke tsakanin shekarun zuwa sakandire. 

Shi kansa wannan lissafi da aka fitar ya nuna yadda adadin yake a ɓangaren kudanci da arewacin ƙasar nan, inda aka nuna a yankin Arewa ne ake samun adadin yara mafi yawa da ba sa zuwa makaranta, musamman a jihohi irin su Sakkwato, Kebbi, da Yobe. Daga cikin dalilan da ake dangantawa da musabbabin wannan matsala akwai batun talauci, ƙalubalen tsaro da kuma riƙon sakainar kashi da wasu gwamnatocin jihohi ke nunawa akan harkokin da suka shafi ci gaban ilimi.

ƙaruwar ayyukan ta’addanci a akasarin jihohin Arewa da sace-sacen ɗalibai ’yan makaranta don neman kuɗin fansa, wanda ya zama ruwan dare a shekarun baya-bayan nan, ya ƙara taimakawa wajen ƙaruwar janye yara daga zuwa makaranta. Babu mamaki yadda ƙiyasin da Hukumar UNESCO ta fitar ya nuna cewa yara mata sun fi yara maza rashin zuwa makaranta a Arewa, saboda dalilai masu nasaba da auren wuri, zuwa aikatau, tallace-tallace, da kuma fargabar yin garkuwa da su. Domin bincike ya nuna cewa daga cikin adadin ɗaliban da ake sacewa ko a yi garkuwa da su yara mata sun fi yawa. Tun daga kan ’yan matan Chibok, Dapchi, Yawuri, da sauran su; ga kuma na baya-bayan nan ’yan makarantar sakandire a Jihar Kogi da aka sace suna tsakiyar rubuta jarabawar kammala sakandire ta NECO. ɓatagari sun mayar da satar mata ’yan makaranta hanyar samun kuɗaɗe masu kauri daga wajen gwamnati. 

A Jihar Filato, babban ƙalubalen da harkar ilimi ke fuskanta ba game da masu garkuwa da ɗalibai ba ne, duk da kasancewar akwai ƙalubalen rikice-rikicen ƙabilanci da na addini a wasu sassan jihar, amma abin da ya fi janye yara daga zuwa makaranta shi ne aikin haƙar kuza da sauran ma’adinai, waɗanda ke kawo wa iyali kuɗi sosai. Don haka yara maza da mata ke komawa ƙauyuka da lungunan da ake yin waɗannan ayyuka suna aikatau don neman kuɗi da biyan buƙatun rayuwa.

Gwamnatin jihar ta bakin Kwamishinan Ilimi Dakta Kachallom Gang ta nuna matuƙar ɓacin ranta da wannan halayya wanda ta ce yana jawo wa gwamnati asara mai yawa, domin kuwa gwamnati na iyaka ƙoƙarin ganin ta gyara gine-ginen makarantu da samar da kayayyakin koyarwa, horar da malamai, da inganta albashin su, amma kwalliya ta kasa biyan kuɗin sabulu. A maimakon iyaye su ba da himma kan ganin ’ya’yansu sun samu ilimi mai inganci, sai ga shi suna janye su daga makaranta don biyan buƙatun kansu.

Kachallom Gang ta bayyana yiwuwar gwamnati ta ɓullo da wani tsari na hukunta iyayen da suka yi kunnen uwar shegu kan mayar da yaransu makaranta. Sannan kuma a duba yiwuwar dawo da tsarin ciyar da ɗaliban makarantun firamare, da farfazowa tare da inganta tsarin makarantun kwana a jihar. 

A ƙoƙarin ganin an dawo da martabar ilimi da kuma dawo da hankalin yara zuwa makaranta, wasu masana harkar ilimi na ganin zai yi kyau sosai a ɓullo da tsarin koyar da yara da yammaci ko a buɗe makarantun boko na dare, da kuma a samar da tsarin makarantun zagaye, ana zuwa ƙauye-ƙauye ana buɗe ajujuwa na wucin gadi, duk dai don a bai wa yara damar samun ilimi, ba tare da an takura musu ko hana su neman kuɗin su ba. Kuma hakan zai taimaka wajen samun natsuwa da haɗa hankalinsu a waje guda. Sannan an buƙaci ƙarfafa tsaro a makarantun kwana da waɗanda ke nesa da gari, ta hanyar haɗa gwiwa da jami’an tsaro, da ’yan banga, ƙarƙashin shirin Tsaron Makarantu na Safe School Initiatiɓe.

Babu shakka ilimi shi ne gishirin rayuwa. Kuma babu yadda za a samu cigaba da nasara a yaƙi da tsadar rayuwa da taɓarɓarewar al’amura ba tare da samar da ingantaccen ilimi da manufofi gwamnati masu muhimmanci da za su samu tallafi da goyon bayan ƙungiyoyin al’umma da iyaye ba.

Lallai ne gwamnati ta nuna da gaske take yi wajen kula da ilimi da kyautata makomar yaran ƙasar, waɗanda su ne manyan gobe, waɗanda ƙasa za ta yi alfahari da su idan sun samu kyakkyawan ilimi da tarbiyya. Lallai ne iyaye su yi wa kansu faɗan ta natsu, don mayar da hankali ga tarbiyyar yaransu da kuma ba su ilimi mai inganci ta hanyar mayar da su makaranta da barin su har sai sun kammala karatun su, sun samu samu sakamako mai kyau, da zai taimakawa rayuwar su watarana.

By ukarofi