2027: Kwankwaso ya tabbatar da yarjejeniyar wa’adi guda da Obi a rubuce

Spread the love

A ranar Litinin Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma abokin tafiyar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Rabi’u Kwankwaso, ya ce ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyarsu a zaɓen 2027, Peter Obi, ya amince a rubuce da yarjejeniyar tsarin shugabancin Nijeriya na wa’adin shekaru huɗu kacal.

Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin wata hira da shi a gidan talabijin na Channels.

Rahotanni sun bayyana cewa yarjejeniyar ta tanadi cewa Peter Obi zai yi wa’adi guda ɗaya kacal na shekaru huɗu a matsayin shugaban ƙasa, kafin mulki ya koma yankin Arewa domin cigaba da tsarin daidaito da raba madafun iko tsakanin yankunan ƙasar.

An ruwaito cewa an cimma matsayar ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin haɗa kan manyan jiga-jigan siyasa da kuma samun goyon bayan shugabannin Arewa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Kwankwaso ya bayyana cewa yarjejeniyar ta samo asali ne daga fahimtar juna da kuma burin samar da shugabanci mai adalci da zai haɗa kan al’ummar Nijeriya. Ya kuma nuna kwarin gwiwar cewa Peter Obi zai mutunta alkawarin wa’adi guda ɗaya idan suka samu damar jagorantar ƙasar.

Sai dai har yanzu batun haɗakar siyasar tsakanin bangarorin biyu na ci gaba da jan hankalin masu ruwa da tsaki, yayin da ake sa ran za a ƙara samun tattaunawa da shawarwari kan yadda za a tunkari zaɓen 2027.

Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa duk wata haɗaka tsakanin Kwankwaso da Peter Obi na iya sauya yanayin siyasar Nkjeriya, musamman idan ta samu karɓuwa daga manyan shugabannin yankuna daban-daban na ƙasar.

By Babaji

Leave a Reply